Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutumin da ke yaƙi da 'masu cire maita'
- Marubuci, Jonathan Griffin & Olaronke Alo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Trending, London & Lagos
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Leao Igwe wani ɗan fafutika ne da ke gaba-gaba wajen taimakon waɗanda ake zargi da maita a Najeriya domin tseratar da su daga ƙuncin da suke shiga, wanda har yakan kai su ga kashe kansu.
"Ba zan bari hakan na faruwa ba. Bai kamata mu zauna muna gani ana kashe mutane ba gaira ba dalili ba," in ji Dr Igwe a zantawarsa da BBC.
Bayan kammala karatunsa na digirin digirgir a nazarin addini a shekarar 2017, sai ya ga zama ba ta gan shi ba. Ya yi rubuce-rubuce da dama kan maita, amma sai ya lura saƙonnin ba sa isa inda yake so.
BBC ta ga bidiyon wani faston cocin Pentacostal a Najeriya yana cire maita, abin da Dr Igwe ya zama ruwan dare a ƙasar, inda mutane da dama suka yarda camfi.
Gargaɗi: Wannan rahoton yana ɗauke da wasu bayanai da za su iya ɗaga hankalin masu karatu
Wannan ya sa Dr Igwe ya assasa ƙungiyar wayar da kan waɗanda ake zargi da maita, inda yake amfani da ilimi da tausayi da dalilai wajen nuna musu muhimmancin daina yarda da camfi.
Ayyukan Dr Igwe sun kai har ƙasashen Ghana da Kenya da Malawi da Zimbabwe da wasu ƙasashen.
Daga cikin waɗan da ƙungiyar ta taimaka akwai wani mai suna Jude mai shekara 33, wanda a watan Agusta aka zarge shi da maita, har ya sha dukan tsiya a jihar Binuwe.
Jude wanda mai aikin haɗa gilasai ne, sannan ma'aikacin banki na wucin-gadi, ya ce wata rana yana kan hanyar tafiya aiki ne ya haɗu da wani ƙaramin yaro yana ɗauke da jarkokin ruwa guda biyu, wanda hakan ya sa ya yi tunanin yaba wa ƙoƙarin yaron.
Yaron bai yi farin ciki da yabon ba, amma sai ya yi tafiyarsa.
Kwatsam sai wasu mutane kusan su 15 ciki har da yaron suka biyo Jude suna jifarsa da duwatsu.
"Sai suka far min, suna ƙoƙarin cinna min wuta," in ji Jude.
An zarge shi da sace gaban yaron, zargin da ya ba shi mamaki, kuma ya musanta.
Zargin ɓacewar gaban mutane ba sabon abu ba ne a wasu sassa na yammacin Afirka.
Amma asali, al'amari da ke da alaƙa da cutar Koro, wadda ke da alaƙa da ƙwalƙwalwa.
Cuta ce ta ƙwalƙwala da ke sa mutum ya shiga tsananin fargabar ɓacewar gabansa ko kuma tsananin ƙankance.
Dr Igwe ya ce Jude ya rasa aikinsa a banki saboda zargin.
Sai kuma aka fara yaɗa bidiyon yadda lamarin ya faru a Facebook, inda Dr Igwe ya gani, sannan suka fara bincike.
A WhatsApp, Dr Igwe yana da ɗimbin mutane a zauruka da ya buɗe a jihohi daban-daban.
A cikin zaurukan akwai gomman mutane da yake kira "advocates" wato ƴan gwagwarmaya. Suna yaɗa bidiyon zargin maita da hotuna, sannan su bi kadin lamarin.
"Mun nemi Jude ne, sannan muka tura masa kuɗi domin jinyar raunukan da ya ji. A hankali muka gyara masa tunaninsa," in ji Dr Igwe.
Ƙungiyar ta kuma ƙuduri aniyar ɗaukar nauyin karatun Jude a jami'a, domin ya sake sabuwar rayuwa.
Mutane da dama a Afirka suna rayuwa cikin fargabar maita, da tsoron tasirin da suke da shi.
Ana danganta talauci da cututtula da rashin haihuwa ga maita.
Waɗanda ake zargi kuma sukan shiga damuwa da ƙunci. Yawancin za ka ga ƙananan yara ne da tsofaffi, wasu ma masu taɓin hankali ne, ko nakasassu, waɗanda suke rayuwa cikin tsananin talauci.
Kamar yadda kafar Nigeria Watch, wadda ke bibiyar rikice-rikice ta hanyar tattara rahotannin kafafen watsa labarai ta bayyana, an kashe mutum takwas saboda zargin maita a ƙasar.
Sai dai BBC ba ta da tabbacin sahihancin alƙaluman ba, amma ta kawo wasu rahotanni a baya, inda aka ci zarafin wasu, aka ma kashe wasu saboda zarfin maita a Najeriya da ma wasu ƙasashen.
Dr Igwe ya ce wasu daga cikin fastoci cocin Pentecostal suna ƙara ƙarfafa masu tunanin tasirin camfi da maita, inda suke da tunanin cewa, "duk wani maye yana da haɗari a cikin al'umma, kuma bai cancani wani tausayi ba, don kamata ya yi a kashe shi."
Wasu fastocin sukan shirya tarukan cire maita na musamman, sannan a watan Agusta, wani allon taro mai taken "dole maye ya mutu" ya bayyana.
Lokacin da Dr Igwe ya ga allon a jihar Imo, sai ya rubuta ƙorafe-ƙorafe zuwa ga hukumomi a ƙasar da ma wasu kafofin watsa labarai domin a dakatar da taron, amma ya ci tura.
Har yanzu cocin da ya shirya taron bai amsa buƙatar BBC ta jawabi ba.
Duk da cewa babu wanda ya mutu a taron, amma fito da kalamam "dole maye ya fito" daga coci bai dace ba, in ji Dr Igwe.
Sannan wasu coci-cocin a Najeriya ba sa tare da irin wannan fahimtar.
"Cire maita ya kamata a yi, ba kashe waɗanda suke da maitar ba," in ji Julius Osimen, wani babban fasto a cocin The Global Citizens a Legas.
Mista Osimen ya ƙara da cewa duk wani cocin da yake farautar mayu to bai fahimci saƙon littafin Baibul ba ne.
"Da Yesu ya zo, ya bayyana komai a fayyace. Ba za ka kashe mutane wai don suna da maita ba, cire musu ya kamata ka yi," in ji shi.
Shi kan shi Dr Igwe sau uku yana sha duka a sanadiyar wannan aikin da ya ɗauka wa kansa, sannan iyalansu sun nuna masa fargabarsu.
A Najeriya, laifi ne ka zargi wani ko ka yi yunƙuri ko barazanar kashe shi saboda zargin maita.
Laifi ne da za a iya ɗaure mutum na shekara biyu a gidan yari. Sai dai ba a cika samun wuraren da aka ɗaure mutane ba.
A shekarar 2021, hukumar kare haƙƙin ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta soki take haƙƙin ɗan'adam a sanadiyar zarginsa da maita, amma duk da haka lamarin na ƙara zama ruwan dare a Afirka da India da Papua New Guinea.
"Yaƙi da lamarin na da wahalar gaske. Ba ya cikin al'adunmu kashe tsofaffin mutane, da kashe waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba," in ji Dr Igwe.