Za a yi gwanjon takardar kwantiragin Messi ta farko

Asalin hoton, Getty Images
Za a yi gwanjon takardar kwantiragin da shaharraren ɗan wasan ƙwallon ƙafa Lionel Messi ya fara sanya hannu a ƙungiyar Barcelona kan kusan dallar Amurka dubu ɗari hudu.
Messi ya sanya hannu a takardar a watan Disamban shekara ta 2000 a lokacin da yake da shekaru goma sha uku a duniya, inda ya zama ɗan wasan da ya fi kowane ɗan wasa cin ƙwallaye a Barca.
Takardan kuma na Dauke da sa hannun wani mai bai wa Barcelona shawara kan cinikin 'yan wasa Josep Minguella, da kuma wakili Horacio Gaggioli, wanda ya ba da shawarar cewa a siyo dan wasan na Argentina.
Ya buga wasansa na farko yana da shekaru 16 kuma ya zura ƙwallaye 672 a wasanni 778 a ƙungiyar ta Catalonia.
Yanzu a shekaru 36 da haihuwa, Messi ya lashe kofin La Liga 10 da na zakarun Turai huɗu a Barcelona kafin ya tafi Paris St-Germain a 2021.







