Kocin Ingila Gareth Southgate ya ajiye aikinsa

a

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Ingila Gareth Southgate ya ajiye aikinsa bayan jagorantar tawagar zuwa wasan ƙarshe na gasar ƙasashen Turai karo biyu a jere.

Tawagar ta Three Lions ta sha kashi a hannun Sifaniya da ci 2-1 a wasan ƙarshen da suka buga ranar Lahadi, da kuma wanda Italiya ta doke su a bugun finareti shekara uku da suka wuce.

A ƙarshen shekarar nan ne kwantaragin kocin mai shekara 53 zai ƙare, inda ya ja ragamar ƙasar tasa ta haihuwa wasa 102 cikin shekara takwas.

"A matsayina na ɗan Ingila mai cike da alfahari, taka wa Ingila leda da kuma jagorantar ta alfarma ce a rayuwata," in ji Southgate.

"Hakan ya fi komai a rayuwata, kuma na yi duk mai yiwuwa.

"Amma lokacin sauyi ya yi da kuma buɗe wani sabon babi."

Tun daga 1966 da kocin Ingila Sir Alf Ramsey ya ɗauki kofin duniya, babu wani kocin tawagar ta maza da ya kai ƙungiyar wasan ƙarshe a wata babbar gasa sai Southgate.

Ya kai Ingila manyan gasa hudu, ya kuma kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar Kofin Duniya a 2018 da kuma na kusa da daf da na ƙarshe a 2022.

An matsa masa lamba a wannan gasar, yayin da wasu magoya baya da dama suka yi amannar bai samu ‘yan wasan gaba isassu ba da zai tun kari gasar da su.

Wasu magoya bayan Ingila sun rika jifansa da kofinan roba bayan 0-0 da suka tashi a wasan da suka yi da Slovenia, wanda ya basu damar tsallakawa zagayen ‘yan 16.

Sai dai daga baya sun dawo goyon bayansa lokacin da tawagar ta kai wasan ƙarshe.

“Tawagar da muka je da ita Jamus cike take da matasan ‘yan wasa masu hazaƙa da za su iya cin wannan gasar, kuma hakan ne mafarkinmu mu duka,” in ji Southgate.

“Mu ke da manyan magoya baya a duniya, kuma nasararmu na tare da goyon bayansu. Ni magoyin bayan Ingila ne kuma haka zan kasance ko da yaushe.

“Ina godiya Ingila – Na gode da komai da aka yi min.”

Tarihin da Southgate ya kafa a matsayin kocin Ingila

a

Asalin hoton, Getty Images

Gather Southgate ya ja ragamar Ingila zuwa wasanni 102 ya kuma yi nasara a wasanni 61, wato ya samu kashi 59.8 cikin ɗari .

Sauran wasanni 41 kuma, Ingila ta yi canjaras 24 sannan ta yi rashin nasara a wasanni 17.

Shi ne koci na uku a tarihin Ingila da ya fi ƙoƙari, ko da yake sauran masu horaswar biyu sun fi shi jan ragamar tawagar yawan wasanni.

Duka wasannin ƙarshe da Ingila ta je a gasar Euro Southgate ne ya kai ta, gabanin shi babu wani kocin tawagar maza ta ƙasar da ya samu wannan nasara.

Shi ne mai horaswa na uku da ya dauki Ingila sama da wasanni 50 kuma yana cikin wadanda suka fi samu kaso mai yawa na nasara a ƙasar.