Ku San Malamanku tare da Malam Abulfathi Attijani
A wannan makon, filinmu na Ku San Malamanku ya tattauna da Malam Abdulfathi Sani, wanda ake yi wa lakabi da Attijany ɗan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya.
Malamin ya shaida wa BBC Hausa cewa an haife shi a unguwar Bakin Kura da ke tsakiyar birnin Bauchi.
Malam Abulfatihi ya yi karatunsa na Al’kur’ani da na Firamari a birnin, tun daga farkon rubutu har zuwa sauke Alkur’ani.
Ya yi karatun Firaimari a Federal Poly Staff School, inda ya dagktar da karatun a shekarar 2003 sannan ya soma karatun Sakandari a College of Arabic and Islamic Studies duk a Bauchi.
Daga nan ne ya samu gurbin karatu a Jami’ar Bayero da ke Kano, inda ya kammala a shekarar 2015. Yanzu haka kuma yana digirinsa na biyu a Jami’ar Jos.
Malamin ya yi karatun Al’kur’ani wurin ‘ya’yan Maulahul Shehu Al’amin da almajiran da ya taso tare da su a gida daya. Bangaren Fiqihu da Larabci kuma ya karance su wurin mahaifinsa.
Malamin ya ce ya tasirantu da mahaifinsa sosai, tare da Maulahul Shehu Al’alamin, ta bangaren da'awa kuma ba zai taba mantawa da Sheikh Usman Bauchi.
Attijjany ya ce ya rubuta littafai na wakar Larabci da dai sauransu da dama amma har yanzu ba a samu buga su ba. Ya kuma kara da cewa ya je garuruwa biyu a cikin Najeriya domin neman ilimi.
Abin malam ya ce ba zai taba mantawa da shi ne lokacin da ya sauka a Madinar Manzon Allah (SAW), "da na hango Alqubbatul kadra wannan koriyar kubbar sai na ji kaina yana juyawa, kamar mafarki, ni din ne ko ba ni din ba ne, sai na ji gabadaya na canza."
Raddi
Malam ya ce ya fara raddi ne saboda irin akidun da suka fara shigowa Najeriya, "kuma Musulman Najeriya sun ginu ne a kan akida ta Asshariya Mazamiya Malikiya, yanzu kuma an samu wasu akidu da suke so su canza mutane, don hakka na fara raddi don kawar da shubahar da ake so a sa a zukatan Musulmai."
Da kuma mutanen da suke ganin cewa 'yan ɗariƙa mutanen banza ne, raddin da yake yi na koyar da mutane cewa akwai mutanen kirki a cikin 'yan tariqa.
Malam Abulfatihi ya ce babu abin da ya fi so kamar Annabi Muhammad SAW
Iyali
Malam Abulfatihi ya ce yana da mace guda da ‘ya daya.
Abinci
Malamin ya ce yana cin kowanne irin abinci amma babu kamar tuwo.



