Ko City za ta karasa binne Bayern a Jamus a Champions?

An wallafa

Bayern Munich za ta karbi bakuncin Manchester City a wasa na biyu a quarter finals a Champions League ranar Laraba.

A makon jiya City ta doke Bayern Munich 3-0 a wasan farko a Etihad a gasar ta zakarun Turai ranar Talata 11 ga watan Afirilu.

Rodrigo Hernandez ya fara cin kwallo a minti na 27 da take leda, Bernardo Silva ya kara na biyu, sannan Erling Haaland ya ci na uku.

Haaland ne kan gaba a yawan cin kwallaye a Champions League a kakar nan mai 11 a raga kawo yanzu.

Ruud van Nistelrooy shine mai tarihin cin kwallo 12 a Champions League mai buga Premier League tsakanin 2002/03.

Kawo yanzu Bayern da City sun buga wasa bakwai a tsakaninsu, kungiyar Premier League ta yi nasara a hudu, mai buga Bundesliga ta ci uku daga ciki.

Wadanda za su iya buga karawar:

Bayern: Sommer; Pavard, De Ligt, Upamecano, Davies; Kimmich, Goretzka; Coman, Musiala, Sane da kuma Muller

Wadanda ba za su buga wasan gaba idan aka ba su katin gargadi: Kimmich, Mazraoui

Man City: Ederson; Walker, Rúben Dias, Aké; Stones, Rodri; Bernardo Silva, De Bruyne, Gündoğan, Grealish; Haaland

Wanda ba zai yi wasan gaba idan aka bashi katin gargadi: Akanji

Tun bayan da Bayern ta sallami Julian Nagelsmann ta maye gurbinsa da Thomas Tuchel, tsohon kociyan Chelsea ya ci wasa biyu ne daga biyar da ya ja ragama.

Haka kuma karawa daya ce ta buga kwallo bai shiga ragar Bayern ba daga bakwai baya da yin wasa biyu a Allianz Arena ba tare da nasara ba.

Kusan shekara uku kenan rabon da Bayern ta kasa cin kwallo a gida, shine wanda ta tashi 0-0 da RB Leipzig a Fabrairun 2020.

Pep Guardiola zai je Jamus da kwarin gwiwa, bayan da City ta ci wasa 10 a jere a dukkan fafatawa.

Haka kuma karawa 14 ta yi ba a doke ta ba, sannan City ta zura kwallo uku a kalla a raga a wasa shida baya.

To sai dai City ta kasa cin wasan waje a Champions League da ta fuskanci kungiyoyin Jamus a kakar nan, bayan wasa da Dortmund da Copenhagen da kuma RB Leipzig.

Guradiola na fatan cin wasa na 100 a Champions League a matakinsa na koci da ya horar a Barcelona da Bayern da kuma Manchester City.

Koci biyu ne suka yi nasara fiye da 100 a Champions League da suka hada da Carlo Ancelotti da kuma Sir Alex Ferguson.

Bayan tashi a wasan farko da City ta doke Bayern Munich a Etihad a makon jiya, an yi fada tsakanin Sadio Mane da Leroy Sane.

Inda ta kai Mane ya naushi Sane daga baya 'yan wasa suka shiga tsakani, inda aka dakatar da mane da cin tara, amma Tuchel ya ce komai ya wuce.