Tsohon kocin Najeriya Rohr ya kara yaga barakar Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kociyan tawagar Najeriya, Gernot Rohr ya cusa wa Super Eagles haushi, bayan da ya doke ta 2-1 ranar Litinin a birnin Abidjan a Ivory Coast.
Hakan ya kara kai koma baya a fatan da Najeriya ke yi don zuwa gasar cin kofin duniya a 2026 da za a yi a Amurka da Canada da Mexico.
Tawagogin sun kara ne a neman gurbi daga Afirka, domin shiga babbar gasar tamaula ta duniya a 2026 a rukuni na uku.
Najeriya ta yi rashin nasara a hannun tsohon kociyanta Gernot Rohr, wanda ya fara aiki da ita a Agustan 2016.
Ya fara da cin wasan farko da doke Tanzania a Uyo, ya fara rashin nasara ranar 10 ga watan Yuni a hannun Afirka ta Kudu da cin 2-0.
Ranar 7 ga watan Oktoban 2017 shi ne na farko daga Afirka da ya samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha a 2018.
Haka kuma ya ja ragamar Super Eagles zuwa mataki na uku a gasar kofin Afirka a 2019, wanda aka kora ranar 12 ga watan Disambar 2021.
An kuma sallame shi duk da kai Najeriya gasar cin kofin nahiyar Afirka a 2021 da karawar cike gurbin shiga gasar kofin duniya.
A ranar ta Litinin Super Eagles ce ta fara cin ƙwallo a minti na 27 da fara tamaula ta hannun Raphael Onyedika.
To sai dai minti 10 tsakani Benin ta farke ta hannun Jodel Dossou, sannan Steve Mounie ya kara na biyu daf da hutu.
A kuma ranar Talata aka karasa wasa na hur hudu a cikin rukuni, inda Rwanda ta je ta ci lesotho 1-0, ita kuwa Afirka ta Kudu ta doke Zimbabwe 3-1.
Da wannan sakamakon Rwanda da Afirka ta Kudu da Benin kowacce tana da maki bakwai, sai Lesotho mai biyar da Najeriya mai uku da kuma Zimbabwe mai biyu.
Duk wadda ta ja ragamar rukuni daga tara da aka raba daga Afirka za ta kai gasar cin kofin duniya kai tsaye.
Daga baya tawaga hudu da suka kare da maki mai kyau a cikin rukuni su kara a wasannin cike gurbi da za a tantance daya daga ciki.
Wasannin da Super Eagles ta buga

Asalin hoton, Getty Images
Ranar 16 ga watan Nuwamba 2023
- Nigeria 1 – 1 Lesotho
Ranar 19 ga watan Nuwambar 2023
- Zimbabwe 1 – 1 Nigeria
Ranar 7 ga watan Yunin 2024
- Nigeria 1 – 1 South Africa
Ranar 10 ga watan Yunin 2024
- Benin 2 – 1 Nigeria
Sauran wasannin da ke gaban Super Eagles
Ranar 17 ga watan Maris 2025
- Rwanda da Nigeria
Ranar 24 ga watan Maris 2025
- Nigeria da Zimbabwe
Ranar 31 ga watan Agustan 2025
- Nigeria da Rwanda
Ranar 7 ga watan Satumbar 2025
- South Africa da Nigeria
Ranar 5 ga watan Oktoban 2025
- Lesotho da Nigeria
Ranar 12 ga watan Oktoban 2025
- Nigeria da Benin










