Chelsea ta dauki Estevao ta fara shirin sayen Anselmino

An wallafa

Dan kwallon Brazil, Estevao Willian zai koma Chelsea da taka leda a kakar badi, yayin da kungiyar ta fara tattaunawa kan daukar dan Argentina, Aaron Anselmino.

Kungiyar Stamford Bridge ta kulla yarjejeniyar daukar Estevao, mai shekara 17 daga Palmeiras kan £29m da karin ladan wasanni, idan ya taka rawar gani.

Dan wasan Brazil, mai shekara 17 ya ci kwallo hudu daga karawa 17 a gasar Brazilian Serie A da Copa do Brasil da kuma Copa Libertadores.

Shi kuwa Anselmino, wanda ake jiran Boca Juniors ta yi masa farashi, ana cewar ya kai darajar £12m zuwa £15m.

Watakila dan wasan mai shekara 19 ya je buga wasannin aro a Strasbourg, wadda take tare da Chelsea mallakin kamfanin BlueCo.

Daukar wadan nan 'yan wasan yana daga cikin tsarin da Chelsea ta shirya na sayen fitattun matasan 'yan kwallon duniya, musamman daga Kudancin Amurka.

Estevao ya bi sawun matasa da Chelsea ta dauka da suka hada da Andrey Santos da Deivid Washington da kuma Angelo Gabriel.

Yayin da matashi mai shekara 17 dan kasar Ecuador, Kendry Paez zai koma Stamford Bridge da taka leda a kakar 2025/26 daga Independiente del Valle.