Masu juna-biyu na fama da ƙarancin abinci mai gina jiki a ƙasashe matalauta – MDD

.

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Asusun kula da ƙananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya ce adadin mata da 'yan matan da ke da juna-biyu waɗanda ke fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki ya ƙaru da kashi 25 cikin 100 a ƙasashe matalauta kamar Somaliya da Habasha da kuma Afghanistan.

UNICEF ya ƙiyasta cewa fiye da mata da 'yan mata biliyan ɗaya a sassan duniya na fama da ƙarancin abinci mai gina jiki.

Asusun ya bayyana cewa matsalolin da aka shiga a duniya shekaru biyu da suka wuce ciki har da yaƙe-yaƙe da kuma annobar Korona su ne suka ƙara ta'azzara shigar mata cikin ƙangin yunwa.

UNICEF ya buƙaci ƙasashen duniya da su sanya batun samar da isasshen abinci a duniya a farko adukkan lamuransu da kuma taimaka wa shirye-shiryen samar da abincin da suka gaza gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

UNICEF ya jaddada irin tasirin da rashin samun abinci mai gina jiki ke da shi kan lafiyar yara.

Rahoton na UNICEF ya gano cewa mata da ƴan mata ba sa samun abubuwan gina jiki daga kalacin da suke yi.

Kudancin Asia da yankin kudu da hamadar Sahara "har yanzu su ne cibiyar matsalar abinci mai gina jiki a tsakanin ƴan mata da mata", in ji rahoton.

Binciken ya kuma ce kashi 68 cikin 100 na mata da ƴan mata ba su kai nauyin da ake buƙata ba, kuma kashi 60 cikin 100 na fama da ƙarancin jini a jiki.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Rashin abinci mai gina jiki a rayuwar mata da ƴan mata na iya raunana garkuwar jikinsu da kuma ƙaruwar hadarin cututtuka da ke barazana ga rayuwarsu - har da lokacin rainon ciki da kuma haihuwa," kamar yadda UNICEF ya bayyana.

Rashin abinci mai gina jiki na iya shafar girman yaro da ƙwaƙwalwarsa da kuma makomarsa a gaba", kamar yadda rahoton ya shaida.

Rahoton ya ƙara da cewa "A faɗin duniya, yara miliyan 51 ƴan ƙasa da shekara biyu a tsumbure suke. Mun yi ƙiyasin kusan rabin waɗannan yaran sun tsumbure ne a lokacin da suke cikin mahaifiyarsu da kuma cikin watanni shidan farko na rayuwarsu, lokacin da yaro ya dogara kacokan kan mahaifiyarsa domin samun abinci mai gina jiki."

A cewar UNICEF, tsakanin shekarar 2020 da 2022, adadin mata masu juna biyu ko masu shayarwa da ke fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki ya ƙaru daga miliyan 5.5 zuwa miliyan 6.9 a ƙasashen 12 da ke fuskantar matsalar abinci.

Ƙasashen su ne Afghanistan da Burkina Faso da Ethiopia da Kenya da Mali da Nijar da Najeriya da Somalia da Sudan da Sudan ta Kudu da Chadi da Yemen.

"Idan har ƙasashen duniya ba su ɗauki matakin gaggawa ba, illarsa na iya kai wa ga al'umma mai tasowa," in ji babbar jami'ar Unicef Catherine Russell.

"Dole ne a magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a tsakanin ƴan mata da mata idan ana son kare rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara," in ji ta.