Keke mai ƙafa uku da mahaya dawaki a cikin hotunan Afirka

Wasu yara

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu yara kenan ke wasan chess ranar Talata a birnin Entebbe na ƙasar Uganda, a lokacin gasar tsakanin makarantun birnin
An wallafa
wasan dominos

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ita ma gasar wasan dominos da aka gudanar a Moroni babban birnin Comoros ranar Asabar ta ɗauki hankali
z

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu matasa kenan ke rawa a bikin al'adar Khousan da aka gudanar a garin Prince Albert na Afirka ta Kudu
a

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Asabar kuma wannan mutumin ke shawagi a kan titin garin na Prince Albert a kan wani keke mai kafa uku da ya kera
a

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An gudanar da bikin bayar da kyaututtuka na makaɗa da mawaƙa a Afirka ta Kudu ranar Asabar, bikin da ya samu halartar mutane da dama daga ƙasashen duniya
d

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Washe gari kuma shahararriyar mawaƙiyar nan 'yar Najeriya Tiwa Savage ta cashe a wajen fadar Windsor Castle a lokacin shagalin bikin naɗin sarkin Ingila Charles lll
ds

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A ranar Juma'a kuma al'ummar Burundi suka tarbi sakatare janar na MDD António Guterres Bujumbura babban birnin kasar lokacin wata ziyara da ya kai ƙasar
g

Asalin hoton, Getty Images

aa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A makwabciyar ƙasar Rwanda mazauna ƙauyen Mubirizi ne suke tono domin zaƙulo ƙasusuwan mutane bayan da suka gano wasu manyan ƙaburburan bai ɗaya a ƙauyen
\

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Tun cikin watan Maris da ya gabata mazauna ƙauyen sun gano gawarwaki fiye da 1,110 na waɗanda aka kashe a lokacin yaƙin basasar ƙasar da ya haddasa kisan kiyashi. A nan mai unguwar ƙauyen ne ke shirya wasu ƙoƙunan kayuwan mutane da aka tono
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Talata kuma wasu ɗalibai ke komawa gidajensu bayan tashi daga makaranta a garin Kibera na kasar Kenya
g

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu mahaya doki a ƙasar Morocco ke bikin tunawa da al'adunsu na Tbourida da suka gada tun ƙarni na 16 a garin Bouznika