Mai jan carbi da masu gangamin siyasa na cikin hotunan Afrika na mako

Mata da miji

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Juma'a kenan inda wani dan kabilar Maasai yake tsaye da matarsa a gaban sabon gidansu a Handeni, Tanzania, bayan da hukumomi suka tashi makiyayan na Maasai daga dajin Ngorongoro suka sauya musu wuri.
An wallafa
Wata budurwa a jikin tsohuwar motar Boksuwaja

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wata budurwa kenan da ta dauki hoto a jikin wata tsohuwar mota kirar Boksuwaja kunkuru, a ranar Lahadi a gidan kayan tarihi na Vintage Africana da ke birnin Lagos na Najeriya.
Wata mata a lambu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Litinin kenan inda wata mata take tafiya a cikin wani lambu da aka samar domin magance tsadar kayan lambu, a babban birnin Ethiopia, Addis Ababa.
wata marubuciya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marubuciya Khadija Abdalla, 'yar kasar Kenya kenan a lokacin da ta halarci bikin duniya na birnin Rum na Italiya a filin wasa na Palatine, ita ma ranar Litinin.
Taron mutane

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, A Kenya kenan ranar Asabar inda wani mutum yake murna a taron siyasa a garin Kisumu, yayin da yake jiran kudin da ake rabawa a wurin, kafin zaben kasar da za a yi a wata mai zuwa.
Makada a wurin murnar cin zaben gwamnan Osun

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Makada da sauran jama'a na murnar cin zaben da dan takarar gwamnan jihar Osun na jam'iyyar PDP, a Najeriya, Ademola Adeleke ya yi.
Wani mutum rike da hotunan 'yan siyasa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani mutum na dauke da hoton dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam'iyyar APC da mataimakinsa, a zaben da za a yi shekara mai zuwa, ranar Laraba a babban birnin kasar Abuja.
Wani mutum a bakin teku

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani dan Senegal da carbi a hannu, zaune a bakin teku a kauyen Djiffer, ranar Talata.
Wani doki a wani masallaci

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wani doki kenan a harabar wani masallaci a garin Palmarin, shi ma a Senegal
'Yan wasan kwallon hannu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Litinin lokacin da wani dan wasan kwallon hannu na Masar zai kai hari gidan 'yan Cape Verde lokacin gasar cin kofin kwallon hannu na Afirka a babban birnin Masar din Alkahira.
'Yan gasar tsere

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nan ma a ranar Litinin ne lokacin gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya a birnin Eugene na jihar Oregon ta Amurka, inda dan Morocco Soufiane El Bakkali ya yi tsalle lokacin gasar da a karshe ya yi nasara. win.
Dan wasan kirket

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dan wasan kirket na Afrika ta Kudu Khaya Zondo yana murna lokacin da tawagarsu ke atisaye a birnin Manchester na Birtaniya.
Dan fim  John Boyega na murna

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, John Boyega kenan dan fim, dan Birtaniya asalin Najeriya lokacin da ya halarci bikin bayar da kyautuka na ESPY a Hollywood ranar Laraba.
Wani mutum da motar kashe gobara

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum na kokarin taimakawa wajen kashe gobara a dajin Borj Cedria da ke wajen babban birnin Tunisia, Tunis, ranar Talata.
Rana na faduwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lokacin da rana ke faduwa a babban birnin Algeria, Algiers, ranar Juma'a.