Modric zai buga wa Croatia Gasar Cin Kofin Duniya karo na hudu

An wallafa

Dan wasan Real Madrid, Luca Modric yana cikin wadanda za su buga wa Croatia gasar kofin duniya a Qatar, kuma karo na hudu da zai wakilci kasar.

Mai shekara 37, shi ne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018, ya kuma je ta Jamus a 2006 da ta Brazil 2014.

Dan kwallon Tottenham, Ivan Perisic da na Chelsea, Mateo Kovacic, suna cikin 'yan wasa 26 da Croatia ta bayyana da za su buga mata gasar ta Qatar.

Za a fara gasar cin kofin duniya tsakanin 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.

Croatia, wadda ta yi ta biyu a Rasha tana rukuni na biyar a Qatar tare da Belgium da Canada da kuma Morocco.

Wasu 'yan wasan da suka yi mata gasar da aka yi a Rasha da yawa za su buga ta Qatar, ta kuma samu karin matasa har da mai shekara 20 mai tsaron bayan RB Leipzig Josko Gvardiol.

Croatia za ta fara wasa a cikin rukuni da Morocco ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba.

Sunayen tawagar Croatia da za ta buga kofin duniya a Qatar:

Masuu tsaron raga: Domink Livakovic (Dinamo Zagreb), Ivica Ivusic (NK Osijek), Ivo Grbic (Atletico Madrid)

Masu tsaron baya: Domagoj Vida (AEK Athens), Dejan Lovren (Zenit St Petersburg), Borna Barisic (Rangers), Josip Juranovic (Celtic), Josko Gvardiol (RB Leipzig), Borna Sosa (VfB Stuttgart), Josip Stanisic (Bayern Munich), Martin Erlic (Sassuolo), Josip Sutalo (Dinamo Zagreb)

Masu buga tsakiya Luka Modric (Real Madrid), Mateo Kovacic (Chelsea), Marcelo Brozovic (Inter Milan), Mario Pasalic (Atalanta), Nikola Vlasic (Torino, on loan from West Ham), Lovro Majer (Rennes), Kristijan Jakic (Eintracht Frankfurt), Luka Sucic (RB Salzburg)

Masu cin kwallo: Ivan Perisic (Tottenham), Andrej Kramaric (1899 Hoffenheim), Bruno Petkovic (Dinamo Zagreb), Mislav Orsic (Dinamo Zagreb), Ante Budimir (Osasuna), Marko Livaja (Hajduk Split)