An ci gaba da yi wa Maguire ihu fiye da wanda aka yi a baya

Harry Maguire

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Luke Shaw ya ce an ci gaba da yi wa dan kwallon tawagar Ingila da Manchester United, Harry Maguire ihu fiye da wanda ake yi masa a baya a fannin tamaula.

Kyaftin din Manchester shi ne ya yi kuskuren da Jamus ta ci kwallo biyu a wasan Nations League da Ingila ta tashi 3-3 ranar Litinin a Wembley.

Ana ta kalubalantar kociyan tawagar Ingila, Gareth Southgate kan gayyatar Maguire da yake yi, wanda United ta ajiye a benci daga baya da fara kakar bana.

Maguire baya kan ganiya a wasannin da yake yi wa tawagar Ingila da Manchester United - an yi wa dan wasan ihu a wasan sada zumunta da Ingila ta doke Ivory Coast a cikin watan Maris.

A cikin watan Afirilu 'yan sanda suka bincike gidan Maguire, wanda wani ya yi masa barazanar dana masa bam - batun ya girgiza mai tsaron bayan United.

Haka kuma an yi wa kyaftin din United ihu a lokacin atisayen kungiyar a Australia - wanda ya buga wasa uku a Premier League ta kakar nan.

Duk da haka kociyan Ingila, Southgate ya ci gaba da bai wa Maguire goron gayyata, domin tsare masa baya, dalilin da ake kalubalantar kociyan kenan.