Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Modric ba zai buga wa Real Madrid wasa da RB Leipzig ba
Real Madrid ta ziyarci RB Leipzig, domin buga wasa na biyar a cikin rukuni na shida a Champions League da za su kara ranar Talata a Jamus.
Real Madrid mai rike da kofin bara mai 14 jumulla tana ta daya a rukuni na shida da maki 10, Leipzig ce ta biyu da maki shida.
Wannan shi ne wasa na biyu da za su buga a tsakaninsu a Champions League, bayan da Real ta ci Leipzig 2-0 ranar 14 ga watan Satumba a Santiago Bernabeu.
Shi ne karon farko da suka fafata a babbar gasar tamaula ta Zakarun Turai a wasan rukuni na shida.
To sai dai Real Madrid ta je Jamus ba tare da Luka Modric ba, wanda tun farko ta bayyana shi cikin 'yan wasan da za ta ziyarci Leipzig.
Haka kuma Real Madrid ba ta fayyace dalilin da dan kwallon Croatia zai zauna a gida ba, wanda kashin bayan kungiyar ne.
Dan kwallon da ke buga gurbin tsakiya ya yi wa Real wasa 14 a bana da cin kwalo hudu da karbar katin gargadi daya.
Ga jerin 'yan wasan Real da suka Jamus karawa da RB Leipzig:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger da kuma F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Camavinga, Tchouameni, Dotor da kuma Arribas.
Masu cin kwallaye: Hazard, Asensio, Vini Jr., Rodrygo da kuma Álvaro.