Kano Pillars ta lallasa Sunshine Stars da ci 5-1

Kano Pillers

Asalin hoton, @Pillersfc

An wallafa

Kano Pillers ta haura zuwa mataki na uku a teburin gasar NPFL ta Najeriya bayan da ta yi wa Sunshine Stars dakan sakwara a wasansu na mako na 22 da aka buga filin wasan Sani Abacha da ke birnin Kano, ranar Lahadi.

Auwalu Ali Malam ya fara jefa ƙwallo a ragar Sunshine cikin minti huɗu da fara wasa, kafin Rabiu Ali ya ci wa Pillars ƙwallo na biyu a minti na 21, hakan aka tafi hutun rabin lokaci.

Da aka dawo wasan ne Ibrahim Mustapha ya ci ƙwallo biyu cikin minti huɗu, kafin Mustapha Umar ya jefa wa Pillars ƙallo na biyar a minti na 55.

Sunshine sun samu bugun fenariti a minti na 81 inda suka samu jefa ƙwallo ɗaya tilo a ragar Pillars.

A wasanta na gaba Pillars za ta kara a wasan hamayya da Katsina United a birnin Katsina, yayin da Sunshine Stars za ta karɓi baƙuncin Lobi Stars wanda ke jan ragamar gasar.