Pogba ba zai buga wa Faransa gasar kofin duniya a Qatar ba

An wallafa

Dan wasan Juventus, Paul Pogba ba zai buga wa Faransa gasar cin kofin duniya a Qatar, bayan da bai murmure daga jinyar gwiwar kafa ba.

Pogba mai shekara 29, bai yi wasa ko daya ba a Serie A ta kakar nan, tun bayan da ya sake komawa Juventus daga Manchester United a kakar nan.

Ya ji raunin a gwiwar kafarsa a cikin watan Yuli, wanda bai amince a yi masa aiki ba a lokacin don gudan kada ya kasa zuwa gasar kofin duniya.

Qatar za ta karbi bakuncin babbar gasar tamaula ta duniya daga ranar 20 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga watan Disambar 2022.

Faransa mai rike da kofin za ta fara wasa da Australia ranar 22 ga watan Nuwamba.

Pogba wanda rabon da ya yi wa Faransa tamaula tun bayan doke Afirka ta Kudu 5-0 a wasan sada zumunta cikin watan Maris, ya koma atisaye a farkon watan jiya.

Amma sai ya kasa motsa jiki yadda ya kamata, hakan ya sa ya yanke shawarar da likitoci su yi masa tiyatar.

Tawagar Faransa ta lashe kofin duniya a Rasha a 2018 tare da Pogba a lokacin.