Me ke faruwa a cikin dutse mafi girma mai aman wuta?

An wallafa

Mauna Loa - wanda shi ne dutse mai aman wuta mafi girma a duniya - ya soma zaɓabbaka tun a shekarar 1984.

Talgen wutan yana ta kwarara ta gefen dutsen a zafin da ya kai digiri 1,000 a ma'aunin celcius, sai dai masana na cewa wannan ba zai kasance wata barazana ba ga mazauna wurin.

Ya girman Mauna Loa?

Mauna Loa, wanda ke nufin "tsauni mai tsawo," da ke Hawaii, shi ne dutse mai aman wuta wanda ya fi aiki a duniya.

Yana da girman murabba'in kilomita 5,271 kuma yana daga cikin duwatsu masu aman wuta biyar da suka samar da tsibiri mafi girma a Hawaii.

Wannan dutsen shi kansa ya ƙunshi rabin tsibirin.

Tsawon Mauna Loa ya kai ƙafa 13,680 a tsayi daga ƙasa zuwa sama, sai dai mazaunin dutsen ya soma ne daga can ƙasa. Daga can ƙasan zuwa sama ya kai ƙafa 30,085 wanda ya sa dutsen ya fi tsaunin Everest girma.

Me ya sa dutsen Mauna Loa ke aman wuta?

Turirin talgen wutar ne yake ci gaba da tashi sama zuwa Mauna Loa da kuma sauran duwatsu masu aman wuta da ke makwaftaka daga can ƙarashin dutsin mai aman wuta.

"Babu wanda ya san asali dalilin da ya sa ke da akwai ƙarƙashin dutsin," in ji Dakta Carmen Solana, wani masanin duwatsu masu aman wuta a Jami'ar Portsmouth da ke Birtaniya, "amma akwai yiwuwar lalacewar

Sai talgen wutan ya soma zuwa daga gefen dutsen da ya tsage inda aman wutar ke tafiya ƙasan tsaunin a matsayin talge. Yana da zafin digiri 1,000 a ma'aunin celcius kuma yana ƙona duk wani abu da ya ci karo da shi.

Idan dutse ya soma aman wuta, dutsen yana fitar da wani abu wanda yake komawa kamar wani gashi da ake kira Pele's Hair.

"Pele sunan wata abar bauta ce wadda ake kyautata zaton ta yi rayuwa a Mauna Loa inda gashin yake da launin ruwan ƙasa da zinare," in ji Dakta Solana.

Me ya sa aman wutar Mauna Loa ke da muhimmanci

Mauna Loa ya yi aman wuta sau 33 tun daga 1843, wanda shi ne lokacin da aka soma rajistar aman wutar.

A taƙaice kenan kamar ana samun aman wutar dutsen sau ɗaya cikin shekara biyar da rabi.

Sai dai aman wuta da dutsen ya yi na ƙarshe ya faru shekara 40 da suka gabata.

"An samu wasu alamu na talgen wutar na zaɓaɓɓaka kusan shekara 10," in ji Andrew Hooper wanda Farfesa ne a Jami'ar Leeds da ke Birtaniya, "sai dai har yanzu dutsen bai soma amayar da wutar ba."

Farfesa Hooper ya bayyana cewa aman wutar Mauna Loa zai bayar da dama ga masana kimiyya na zamani su yi nazari kan yadda ake samun aman wuta.

Shin aman wutar Mauna Loa na da hatsari?

Ba kamar sauran duwatsu masu aman wuta ba, Mauna Loa bai cika fitar da ababe masu fashewa ba, inda talgen wuta ke tashi zuwa sararin samaniya tare da toka da iska.

"Kwararar wutar ba ya barazana ga rayuwa," in ji Farfesa Hooper, " saboda za ka iya kauce musu.

"Haka kuma aman wutar ba ya tafiya yammaci zuwa garuruwan da ke kusa, amma yana tafiya arewa maso gabas. Sai wutar ta yi tafiya mai nisa zuwa wurin kafin ta yi illa ga kayayyaki.

Sai dai mutanen da ke karkara zai iya yi musu illa sakamakon sinadaren iska da ke fitowa daga Mauna Loa.