Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Kashi uku na nau’o'in cutar kansa a Najeriya na kai da wuya ne'
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Masana kiwon lafiya a Najeriya suka ce kashi uku na dukkan nau’o'in cutar kansa da ke kama ‘yan kasar na kai da wuya ne.
Masanan sun fadi hakan ne albarkacin ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin wayar da kan al’umma kan kansar kai da kuma ta wuya.
An kebe duk ranar 27 ga watan Yulin ko wace shekara ce domin jan hankalin mutane su fahimci irin illolin da kansar ta kai da kuma wuya ke haddasawa.
Albarkacin wannan ranar BBC ta tattauna da Dakta Mustapha Abubakar Yaro shugaban asibitin kula da cututtukan kunne na kasa dake Kaduna.
Dakta Mustapha ya ce masu kwankwadar barasa da taba sun fi shiga hadarin kamuwa da nau'in cutar kansar ta kai da wuya.