Waiwaye: Majalisa na son a dakatar da yarjejeniyar Samoa da hukuncin kotun ƙoli kan 'yancin ƙananan hukumomi

An wallafa

Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Kotun Ƙoli ta hana gwamnoni riƙe kuɗin ƙananan hukumomi

A cikin makon da ya gabatan ne Kotun Ƙolin Najeriya ta hana gwamnaonin jihohin ƙasar riƙe kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Cikin hukuncin da kotun ta yanke ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Emmanuel Agim, ya ce kotun ta fahimci yadda gwamnatocin jihohi suka shafe fiye da shekara 20 ba tare da sakar wa ƙananan hukumomin mara ta fuskar kuɗaɗensu ba.

Alƙalin kotun ya ci gaba da cewa tun tsawon wanan lokaci, ƙananan hukumomin ba sa samun kuɗaɗen da ya kamata su samu daga gwamnonin jihohin ba, waɗanda ke kashe kuɗin ta hanyar yin ayyuka a madadin ƙananan hukukomin.

Mai shari'a Agim ya ce dole ne ƙananan hukumomin ƙasar 774 su riƙa amfani da kuɗaɗensu da kansu ba tare da sa katsalandan daga gwamnonin jihohi ba.

Karanta cikakken labarin a nan

Majalisar wakilai ta nemi a dakatar da yarjejeniyar Samoa

A cikin makon da ya gabatan ne dai majalisar wakilan Najeriya ta buƙaci gwamnatin tarayya ta gaggauta dakatar da yarjejeniyar Samoa da ta tayar da ƙura a ƙasar.

A zaman da ta yi ranar Talata, majalisar ta ce ya kamata a dakatar da yarjejeniyar har sai gwamnati ta fito ta bayyana ɓangarorin yarjejeniyar da suka haifar da cecekuce.

Ɗanmajalisar wakilai Hon Aliyu Madaki wanda ya tabbatar wa da BBC da matakin ya ce majalisar ta kuma nemi ministocin da suka jagoranci sanya hannu a yarjejeniyar su gurfana gabanta tare da takardun yarjejeniyar domin buƙatar fayyace komi musamman "ɓangaren da ke bayani kan daidaiton jinsi."

Gwamnatin Zamfara ta taƙaita zirga-zirgar babur a faɗin jihar

A ranar Alhamis da ta gabata ne gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal Dare ya sanya hannu kan dokar taƙaita zarga-zirgar babura a faɗin ƙasar saboda dalilai na tsaro.

"Dokar da gwamnan ya sanya wa hannu ta taƙaita zirga-zirgar babura daga ƙarfe 8:00na dare zuwa 6:00 na safe," kamar yadad yake ƙunshe cikin sanarwa kakkakin gwamnan.

"An umarci jami'an tsaro su hukunta duk wanda aka kama ya saɓa wa dokar," a cewar sanarwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa an ɗauki matakin ne domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma da kuma magance ƙalubalen tsaro da jihar ke fuskanta

Tinubu ya amince da ƙirƙiro hukumar kula da kiwon dabbobi

A ranar Talata ne shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da kafa hukumar kula da kiwon dabbobi, bayan kafa kwamitin shugaban ƙasa da zai kawo sauye-sauyen kiwon dabbobi a fadarsa.

Hakan wani mataki ne na yunƙuri na shawo kan rikicin shekara da shekaru tsakaninn manoma da makiyaya a Najeriya

Tinubu ya ce yana fatan ɓullo da sabuwar ma'aikatar zai kawo ƙarshen rikice-rikicen da aka kwashe shekaru ana samu tsakanin manoma da makiyaya.

''Mutane na cewa za a jima ba kawo ƙarshen matsalar ba, amma ni na ce za a magance ta nan ba da jimawa ba, da dama daga cikinku sun san yadda za a magance matsalar domin ciyar da ƙasarmu gaba,'' in ji shugaba Tinubu a jawabin da ya yi lokacin kafa kwamitin.

Majalisar dattawa ta ɓukaci Tinubu ya duba batun tsadar abinci

Ɗan majalisar Dattawan Najeriya Sanata Ali Ndume, ya shaida wa BBC cewa babbar matsalar da ake fama da ita a wannan gwamnati ita ce kofar su a rufe take yadda hatta wasu ministocin ba sa iya ganin shugaban kasa, bare 'yan majalisa ma su samu zarafin ganawa da shi da bayyana abubuwan da ke faruwa a yankunan da suke.

Sanatan na magana ne jim kadan bayan sun gabatar da wani ƙudurin hadin gwiwa tsakaninsa da takwaransa Sanata Sunday Steve Karimi, suna cewa hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin mutum miliyan 82 za su yi fama da matsalar abinci a Najeriya nan da shekara biyar masu zuwa.

Sanata Ndume ya ce manufar kudurin ita ce, janyo hankalin mahukuntan kasar su san matsalar yunwar da ake fuskanta a Najeriya baki daya, kamar yadda shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi, wanda a bana ne aka sanya Najeriya cikin kasasshen da za su fuskanci yunwa a duniya.