Chelsea na son daukar Ronaldo, AC Milan na zawarcin Ziyech

Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ronaldo
An wallafa

Chelsea na duba yiwuwar dauko dan wasan gaba na Manchester United  Cristiano Ronaldo, wanda ya shaida wa kungiyar yana son barinta a wannan kakar. (Athletic - subscription required)

Ronaldo, mai shekara 37, ka iya komawa Chelsea, sai ai har yanzu Blues ba su yanke shawarar ko su aike wa dan wasan Portugal din takardar zawarcinsa ba. (ESPN)

Mai kungiyar Barcelona,  Joan Laporta  da wakilin Ronaldo, Jorge Mendes, na tattauna kan yiwuwar tafiyar tsohon dan wasan na Real Madrid, zuwa La Liga da wani sabon salo. (AS - in Spanish)

Shi ma Ronaldo din, yana iya amincewa da rage kudin da za a biya shi a kowanne mako, Manchester United dai na biyan dan wasan fam 500,000 a kowanne mako. (Independent)

Chelsea na tattaunawa da Manchester City kan dauko dan wasan gaba na Ingila Raheem Sterling, mai shekara 27, wanda darajarsa ta kai fam miliyan 50. (Sky Sports)

AC Milan na kokarin rattaba hannu don dauko dan wasan Chelsea, asalin Morocco Hakim Ziyech, mai shekara 29, amma a matsayin bashi. (Athletic - subscription required)

Jami’an kungiyar Manchester United za su gana da takwarorinsu na Ajax a karshen mako domin tattaunawa kan daukar mai tsaron gida na Argentina Lisandro Martinez, mai shekara 24, inda aka da tayin sa kan fam miliyan 39.6 (Mirror)

Tottenham na tuntuba kan dauko dan wasan gaba na Netherland da  Barcelona Memphis Depay, mai shekara 28, wanda zai iya barin Nou Camp kan farashin da ya kai fam miliyan 17. (Sport - in Spanish)

Brighton na son dauko dan wasan baya na Argentina, Nicolas Tagliafico, mai shekara 29, wanda Ajax ta amince da saída shi kan fam miliyan 3.3. (Sussex Live)

Nottingham Forest ta amince ta kasha fam miliyan 13, domin dauko mai tsaron baya na Faransa  Moussa Niakhate, mai shekara 26, daga Mainz. (Mail)

West Ham ta sanya fam miliyan 20, a kokarinta na daukar dan wasan tsakiya na Belgium Amadou Onana, mai shekara 20, wanda Lille ta yi watsi da shi. (Athletic - subscription required)

Crystal Palace, da Southampton da Nottingham Forest na son dauko tsohon matashin dan wasan tsakiya na Ingila Morgan Gibbs-White, mai shekara 22, daga Wolves. (Mail)