Man City na son Gakpo, United za ta raba Myles Lewis-Skelly da Arsenal

    • Marubuci, Muhammad Annur Muhammad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City ta shiga jerin kungiyoyin da ke son sayen dan wasan gaba na Liverpool da Netherlands, Cody Gakpo, mai shekara 27. Tottenham ma na ci gaba da kokarin kulla yarjejeniya da dan wasan. (Soccer News NL - in Dutch)

Newcastle ta cimma yarjejeniyar baka da Manchester City kan sayen dan wasan tsakiya na Sifaniya, Nico Gonzalez, mai shekara 24, kan fam miliyan 47 tare da karin fam miliyan uku da ke da alaka da cika wasu sharudda. (Fabrizio Romano)

Manchester United na da kwarin gwiwar cewa za ta iya shawo kan Arsenal ta sayar mata da dan wasan Ingila, Myles Lewis-Skelly, mai shekara 19. Sai dai farashin da Arsenal ta sanya masa, wanda ya haura fam miliyan 50, na ci gaba da zama wani babban kalubale a tattaunawar. (Sun)

Newcastle ta gabatar da tayin yuro miliyan 40, kimanin fam miliyan 34.2, ba tare da kari ba, domin sayen dan wasan gaba na Lille da Belgium, Matias Fernandez-Pardo, mai shekara 21.(L'Equipe - in French)

Chelsea ta yi tayi har sau uku a wannan bazarar domin sayen dan wasan tsakiya na Bournemouth da Ingila, Alex Scott, mai shekara 23, amma Bournemouth ta yi watsi da dukkan tayin. (The i)

Hull City ta gabatar da tayin yuro miliyan 21, kimanin fam miliyan 17.9, domin sayen dan wasan gaba na Union Berlin kuma dan wasan tawagar Jamus ta 'yan kasa da shekara 21, Ilyas Ansah. Tattaunawa kan kwantiragin dogon lokaci na ci gaba da samun nasara. (Sky Deutschland - in German)

AC Milan na nazarin yiwuwar daukar dan bayan Manchester United da Morocco, Noussair Mazraoui, mai shekara 28, kafin rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa. (CaughtOffside)

Coventry City ta amince da yarjejeniyar fam miliyan shida domin sayen dan bayan Brentford da Jamaica, Ethan Pinnock, mai shekara 33. (Athletic - subscription required)

Kungiyar Monza ta Italiya na shirin bai wa tsohon dan wasan Tottenham da Ingila, Dele Alli, mai shekara 30, kwantiragin shekara daya. Alli ya kasance ba tare da kungiya ba tun bayan barinsa Como a watan Satumban 2025. (Fichajes - in Spanish)