Muhimman sarautu 7 da ake ba mata a ƙasar Hausa

    • Marubuci, Khalifa Shehu Dokaji
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

A tarihin masarautun ƙasar Hausa, mata ba ƴan kallo ba ne kawai a tsarin yadda ake gudanar da mulki, suna taka muhimmiyar rawa a harkokin fada da shi kansa gidan sarauta, ta hanya daban-daban da aka tanadar musu.

Wasu daga cikin waɗannan sarautu sun shafi shugabanci a harkokin da suka shafi iyalan sarki da harkokin cikin gida, sai ɓangaren bayi da baƙin da suke neman iso don ganin sarki.

Duk da cewar a yau wasu daga cikin waɗannan mukamai sun ragu ko kuma sauyin zamani ya yi tasiri a kansu, tarihin ya nuna cewar mata sun kasance ginshiƙi mai ƙarfi a tsarin tafiyar da harkokin masarautu, da sauran al'amuran cikin gidan sarakuna tsakanin mata bayi, da su kansu iyalai, da ƴaƴan sarki maza da mata.

A cewar Dr. Nasir Wada Khalil, masanin tarihi kuma mai bincike a jihar Kano da ke Najeriya, ya ce 'sarautun mata a gidan sarauta sun kasu gida uku.

  • Sarautun da suka keɓanta ga 'ya'yan sarki mata,
  • Waɗanda suke bayi za su iya, ƴaƴan sarki za su iya yi.,
  • Waɗanda ake bai wa mata daga cikin bayin sarki da ke gudanar da harkokin su na yau da kullum, a cikin gidan sarki.

Sarautun Ƴaƴan Sarki:

Sarautun da aka san ƴaƴan sarki mata na musamman a masarautar Kano guda biyu ne.

  • Magajiyar ƴaƴan sarki
  • Kilishi

Sai dai kuma a cewar Dr Nasir Wada Khalil "a wasu lokutan akan sami mutum guda ya zama Kilishi kuma Magajiya."

Hakan ya sha bamban da wata masarauta, duk da cewar sarki na da ikon yin ƙarin wasu naɗe-naɗe ga ƴaƴansa, na wasu sarautun "amma waɗanda aka fi sani su ne waɗannan biyun" a cewar Dr Nasir wada Khalil.

Magajiyar ƴaƴan Sarki

Sarautar Magajiya na daga cikin manyan sarautun da ake bai wa mata a masarauta. A al'ada, babbar ƴar sarki ita ce ke riƙe da wannan sarauta.

Dr. Nasir Wada Khalil, ya ce Magajiya ita ce shugabar dukkan 'ya'yan sarki mata.

Haka kuma ya ce ita ce ke kula da harkokin zumunci da dangantaka tsakanin sassan gidan sarauta, tare da taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan dangi.

"Ta kan sa takalmin gashin jumuna, da wasu daga cikin kayan sarauta," In ji Dr Nasir Wada Khalil.

Sannan kuma masanin tarihin ya ce ita "kalmar Magajiya ba sabuwar kalma ba ce. Kalma ce da aka dade ana amfani da ita a tsarin shugabanci da gado a ƙasar Hausa. Kamar yadda ake da Magajin Gari ko Magajin Banga, haka ma Magajiya ke nuni da shugabanci da jagoranci", in ji masanin tarihin.

Sai dai ya ce wasu sabbin fassara da ake danganta sarautar Magajiya da wasu rukunin jama'a ba haka asalin sarautar take ba a tsarin gidan sarauta.

Dr Nasir Wada Khalil ya ce "saɓanin Magajiya, ba a kiran babban ɗan sarki da laƙabin Magaji."

Kilishi

Abin lura shi ne, sarautar Kilishi ba ta tsaya ga mata kawai ba.

Sai dai Dr. Nasir Wada Khalil ya ce "Namiji ko mace na iya amsa sunan Kilishi muddin an haife shi ne bayan hawan mahaifinsa mulki.

Idan kuwa sarki bai samu haihuwa ba sai bayan ya zama sarki, kuma aka fara haifar mace, to ta na iya zama Kilishi" a cewar masanin tarihin.

Sannan masanin tarihin ya ce mutum guda na iya haɗa sarautun biyu, na Kilishi da na Magajiyar ƴaƴan sarki.

Baya ga sarautu, akwai wasu sunaye na girmamawa da ake kiran mata a cikin masarauta.

A wasu gidajen sarauta, ana kiran 'ya'yan sarki mata da Fulani. Sai dai ba a amfani da wannan suna ga yarinya har sai ta kai ga ta yi aure.

Masanin tarihin ya ce "bayan aure, ana iya kiran ta Nani ko Gwaggo, gwargwadon matsayinta a cikin gida", in ji Dr Nasir wada Khalil.

Haka kuma ya ce su kuwa matan da suka taso daga cikin bayin sarki, bayan aure ana kiran su Yaya, wanda ke nuna matsayinsu da darajarsu a tsarin fada.

Mai Babban Ɗaki

Ita kuma Sarautar Mai Babban Ɗaki na ɗaya daga cikin sarautun mata da matan aure na yi kuma bayi na iya yinsu saboda Sarauta ce ta mahaifiyar sarki.

Dr Nasir Wada Khali ya ce "idan mahaifiyar sarki kuyanga ce, to ta zama Mai Ɓabban Ɗaki, idan kuma, dan matar aure ne ya zama sarki, ta zama Mai Babban Ɗaki.

Wannan sarauta tana nuna matsayi na girmamawa da darajar da mahifiyar sarki a tsarin masarautar.

Tsarin Sarautun Mata Bayi

Sarautun mata bayi a masarautun Kano kamar yadda Dr Nasir Wada Khalil ya ce a tsarin sarautun da mata bayi ke yi sun haɗa da:

  • Uwar Soro
  • Uwar Waje
  • Mai Soro Baƙi
  • Mai Kudandan
  • Jakadiya

Uwar Soro

Uwar Soro ita ce shugabar dukkan mata bayin sarki, da ke cikin gidan sarki.

Ita ce shugabar mata masu kula da al'amuran fada. Kullum tana karɓar rahotanni daga sauran shugabannin mata tare da miƙa muhimman bayanai ga sarki.

Dr Nasir wada Khalil ya ce "ana iya kwatanta matsayinta da shugaban majalisar mata a gidan sarki, domin duk wata matsala ko buƙata da ake da ita ko ta taso daga ko'ina acikin gidan sarki, sai ta bi ta hannunta kafin ta kai ga isa gaban sarki."

"Sannan tana zaune ne a Unguwar Yalwa da ke gidan sarkin Kano, sannan takan zauna tare da dukkan sauran manyan bayi mata da ke fada a dukkan safiya inda suka bayar da rahoton abubuwan da suka faru a cikin dare zuwa safiya sannan ita kuma ta sanar da sarki," in ji Dr Nasiru Wada Khalil.

Har ila yau ya ce wani abu da ba za a taɓa manta wa da shi ba game da masu riƙe da ko waɗanda suka taɓa riƙe sarautar ta Uwar Soro, shi ne yadda ta taɓa saukar sarauniyar Ingila a sanda ta zo kano.

"A tarihin Kano, an samu shahararriyar Uwar Soro mai suna Hadiza Wayo, wadda kaka ce ga sarkin Kano na yanzu wato Muhammad Sanusi II ce, inda ta yi abun da ba a taɓa yi ba, sannan hakan ya sa ta yi fice har ta samu damar jagorantar karɓar sarauniyar Birtaniya tsawon minti 30, a yayin wata ziyara da ta je Kano," a cewar Dr Nasir Wada Khalil.

Mai Soron Baki

Yaya Mai Soron Baki ita ke bin Uwar Soro, wadda ke taka muhimmiyar rawa a harkokin da ke bi a je gaban sarki.

Duk wanda zai ga sarki, ko ɗan gida ne, baƙo ne ko kuma wani mai neman wata buƙata ne a gaban sarki, tilas ne a bi ta hannun ta.

Dr Nasir Wada Khalili ya ce "ita ke tsara lokacin shiga da kuma tabbatar da cewa komai yana gudana cikin tsari, shi ya sa ɗakin ta yake a bakin hanya, ta yanda tana ganin dukkan abun da ke kaiwa da komowa a da wanda ya shiga da wanda ya fita daga gidan sarki."

Haka kuma ya ce takan yi aiki tare da Uwar Soro kusa da kusa, wanda takan zama tamkar mataimakiyarta.

Sannan duk wanda ke son ganin sarki, ko baƙo, ko ƴaƴa, ko ƴan uwan sarki, kai ko wanene ita ce ke yi musu iso wajen sarki.

Uwar Waje

Wanda ke biyewa Mai Soron Baki ita ce Uwar Soro, wadda ita kuma ita ke kula da dukkanin unguwanin da ke cikin gidan sarkin Kano.

Akwai dai unguwannin masu yawa a cikin gidan sarki, kuma kowace unguwa tana da wadda ke shugabantar da ke ƙarkashin ta wanda hakan ya sa ake kiranta da Uwar Waje.

A cewar Dr Nasir Wada Khalil "ita ce ke da alhakin sanin halin da mutanenta suke ciki, da abubuwan da ke tafiya a kowacce unguwa da ke cikin gidan sarki."

Haka kuma dukkan dogarai mata da ke irin wannan unguwanni da ke gidan sarkin na kawo mata rahotonnin wanda ba shi da lafiya, da wanda ya yi tafiya, da wanda ko wacce ba ta kwana a gida ba, wato dai dukkan abun da ya wakana a kowacce unguwa da ke gidan sarkin,' a cewar Masanin tarihin.

Idan akwai saƙo daga fada zuwa jama'ar unguwar, ita ce za ta isar.

Sannan idan mutanen karkashinta suna da wata buƙata, ta hannunta ne za ta kai ga sanar da mai Uwar Soro ita kuma ta sanar da sarki, wanda lamarin ya shafa.

Mai Kudandan

Mai Kudandan na ɗaya daga cikin muhimman sarautun fada, wanda kuma aikinta shi ne rabon abinci.

Dr Nasir wada Khalil ya ce "ita ce za ta bayar da hatsi ga 'yan turmi su kuma su sarrafa shi, bayan an sarrafa hatsin, ko nau'in abinci, idan an gama ita ce za ta zo ta raba abinci su kuma 'yan daka, sai su ɗauka su kai gurin uwar waje, ita kuma ta rarrabashi zuwa unguwanin da ke gidan sarkin" a cewar masanin tarihin.

Haka kuma ita ke kula da ƴan daka (masu daka, da surfe da girka abinci ), kuma ta san adadin mutane da ke kowane waje ‘unguwanni).

"Kasancewar akwai unguwani kamar Sokoto, Katsina , Nasarawa, Garko Sararin Garke, bayan Ɗan Soro, Yalwa, Asibiti, da makamantansu, wanda hakan ke basu damar sanin adadin mutanen da ke kowacce unguwa, da yawan abincin da za a kai jusu", a cewar Dr Nasir Wada Khalil.

Jakadiya

Idan za ka yi magana kan sarautun da bayi mata ke yi dole sai ka fara ta 'Kuyanganci', wanda ke nufin 'yarinyar baiwa'.

Wanda a nan baiwa irin waɗannan kuyangi sarautar Jakadiya, ko da kuwa wani dalili ya sa ta yi aure a waje, ko kuma ta dawo gida bayan auren na ta ya mutu.

Dr Nasir Wada Khalil ya ce 'Jakadiya wata sarauta ce da ake baiwa wasu daga cikin matan fada bayan sun kai wani matsayi.

"Haka kuma aikin Jakadiya ya fi karkata ga aike, ko isar da saƙo, sai gudanar da wasu ayyuka na wakilci da taimakawa a harkokin hulɗa tsakanin sarki da wasu ɓangarori, na cikin gidan sarki da suka shafi aikatau, ko aike," a cewar masanin tarihin.