Man Utd na son Hjulmand, Tottenham na fatan ƙulla yarjejeniya da Eze

Morten Hjulmand

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Morten Hjulmand
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na shirin biyan fan miliyan 50 kan dan wasan tsakiya na Sporting da Denmark Morten Hjulmand, mai shekara 26, idan har ta rasa dan wasan Brighton dan kasar Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 21. (Sun)

Tottenham na da kwarin gwiwar cewa za ta kulla yarjejeniya da Eberechi Eze, mai shekara 27, wadda za ta gamsar da Crystal Palace, mai neman fan miliyan 68 kan dan wasan tsakiya na Ingila .(Teamtalk)

Fulham da AC Milan na sha'awar dan wasan gaban Manchester United da Denmark Rasmus Hojlund, mai shekara 22. (Mail)

Chelsea na samun ci gaba a kokarinta na sayen dan wasan gefe na Manchester United, Alejandro Garnacho, mai shekara 21, kuma ta yi imanin fam miliyan 35 farashi ne mai kyau ga dan wasan na Argentina. (Teamtalk)

Arsenal na shirin duba tayin da aka yi wa dan wasan baya na Ukraine, Oleksandr Zinchenko, mai shekara 28, inda Porto da Fenerbahce da kuma Real Betis ke son su dauko shi .(CaughtOffside)

Brentford ta kosa ta dauko dan wasan Burkina Faso Dango Ouattara, mai shekara 23, amma ya zama dole ta jira saboda sai Bournemouth ta samu wanda zai maye gurbinsa kafin cinikin ya kankama.(Guardian)

Borussia Dortmund ta bi sahun Bayer Leverkusen wajen nuna sha'awar daukar dan wasan gefe na Brighton da Argentina Facundo Buonanotte, mai shekara 20, matsayin aro a kakar wasa ta bana.(Mail)

Inter Milan za ta ba da mako guda don kokarin kammala siyan dan wasan gaban Najeriya Ademola Lookman, mai shekara 27, daga Atalanta kafin hankalinta ya koma wurin sauran 'yan wasa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Roma ta yi wa Inter Milan tayin dan wasan tsakiyarta Manu Kone, inda take neman kusan euro miliyan 30 kan dan wasan Faransa mai shekaru 24.(Gazzetta dello Sport - in Italian)

Liverpool ta yunƙura kan neman sayen dan wasan bayan Parma Giovanni Leoni mai shekara 18.(Sky Sports Italia - in Italian)