Yadda ake samun ƙaruwar masu ƙarzuwa a Kano

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Ƙarzuwa wata cuta ce ta fata wadda aka fi samunta fiye da sauran cututtukan fata a kasashe masu tasowa, kuma ta na shafar mutane fiye da miliyan 400 duk shekara, a cewar Hukumar lafiya ta duniya.

Hukumar ta bayyana cewa cuta ce wadda wasu 'yan mitsi-mitsin ƙwari da ba a iya gani da idanu ke janyowa, wadanda ke huda fata su maƙale a ciki su yi ƙwayaye.

Hakan na janyo matukar kaikayi da kuma kananan kurarraji.

Sannan an fi samunta a ƙasashe masu tasowa, waɗanda kuma ke da yanayi na zafi, kamar irin su Najeriya.

A baya bayan nan, ƙwararru a fannin lafiya a ƙasar sun soma nuna damuwa game da abin da suka kira 'matukar ƙaruwar yaɗuwar cutar'.

Kwararren likitan fata, farfesa Shehu Mohd Yusuf wanda ke aiki a asibitin koyarwa na Aminu kano da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, ya ce cutar na ƙaruwa sosai tsakanin alumma a jihar ta Kano, kuma akwai buƙatar ɗaukar matakai.

Ya ce mutane dayawa na kamuwa da ƙarzuwa a yanzu idan aka kwatanta da shekarun baya, '' a yanzu idan na ga mutum goma, toh mutum uku na ɗauke da cutar' in ji shi.

Likitan fatan ya kuma hakan ba ya rasa nasaba da rashin wayewar wasu mutanen, da rashin fahimtar ita kanta cutar da kuma halin rayuwa a yanzu.

'' A yanzu alummar jihar sun ɗan ƙaru, ga matsin rayuwa, ko a gida za ka ga ɗaki ɗaya da yara biyar ko fiye, hakan na taimakwa wajen yaɗuwar ta.

Ko makaranta ka je yanzu, a baya a aji ɗaya za ka ga mutum sha biyar ne, yanzu aji mutane 30 ko arbain ko ɗari ne a ciki, idan ɗaya na da Kazuwa zai shafa musu, shi ma yaron idan ya je gida zai shafa wa ƴan uwansa, dole ne a samu ƙaruwar yaɗuwar ƙarzuwa.'' in ji farfesa Shehu.

Likitan ya kuma yi ƙarin bayani kan cutar, da alamominta :

Ƙaikayin jiki ne alama ta farko, kuma ya fi ta'azzara ne da daddare, sannan a kan same shi a kowane sashe na jiki.

Ya kuma ce daga nan sai ƙananan kuraje su fito, idan ba a yi magani ba, sai su fashe su fara ruwa, ko su bushe, har fatan ya yi tauri.

Farfesan ya kuma ce an fi samun kurajen ne a wasu gaɓoɓi, kamar tsintsiyar hannu, da gwiwar hannu, da kasan nono, da hammata, da idan sahu, ko gwiwowi, ko kuma mazauni, 'akasarin lokuta ma in dai mutum na da kuraje masu ƙaiƙayi, har a mazauni to ba mamaki Kazuwa ne' in ji shi.

Ya kuma ce cuta ce da kan kama kowane mutum, ba tare da la'akari da shekarun sa ba. Hakazalika akan same ta a kowane yanayi, na sanyi ko zafi.

'Ba kazanta ke kawo ƙarzuwa ba'

Farfesa Shehu ya kore tunanin da ake yi na cewa kazanta ke kawo cutar inda ya ce wasu ƙwayoyin cuta ne kawai ke kawo ƙarzuwa, kuma ana iya samunsu a ko ina, sannan da zarar mutum ya kamu zai iya yaɗawa.

Sai dai ya ce yawanci masu kazanta su kan taru waje ɗaya ne, suyi amfani da kaya daya, don haka zai yaɗu da wuri a tsakaninsu, amma ba kazantarsu ce ta kawo ba.

'Za ka ga mai sarauta da ƙarzuwa, ko ni na ga babban dan siyasa da ita' in ji Farfesa.

Ya kuma ce za a iya samu a ko ina, wani lokacin idan mutum ya zauna a wurin da wani mai ita ya zauna zai iya kamawa, ko mutum ya ɗauki hula ko rigar wani mai cutar ya saka, ko wani ya kwanta a inda mai ƙarzuwa ya kwanta ko da kuwa hotel ne to zai ɗauka.

'Cuta ce mai saurin yaɗuwa'

Farfesa Shehu Muhammad ya ce idan mutum ɗaya a gida ya zo da ita, dole ne sai kowa a gidan ya yi magani, daga yaran gidan har masu aiki a gidan, idan ba haka ba maganin ba zai yi tasiri ba.

Ya ce idan mutum ɗaya kawai aka yi wa, za ta yiwu shi kuma ɗayan tana jikinsa amma sai bayan sati biyu za ta bayyana, to a wannan lokacin zai yi ta yaɗa ta.

A cewar sa, da zarar an tsallake mutum ɗaya wajen magani, to ciwon zai ci gaba da yaɗuwa, har ya fita ya bar wannan gidan ya tafi wani wuri ma.

Ya kuma ce hakan ne yasa mafi yawan lokuta ta kan yaɗu sosai a makarantu, ''da zarar yaro ɗaya na da cutar, ganin cewa suna yawan zama a wuri daya, zai yi ta yaɗata a faɗin makarantar.'' in ji shi.

Hanyoyin kauce wa yaɗuwarta

Ƙwararren likitan fatan da ke Kano ya ce ƙarzuwa ba cuta bace da ake yi wa rigakafi ba, amma kuma ana iya kauce mata ko yaɗuwarta.

Ya ce hanya mafi sauki da za a kauce wa yaɗuwar cutar shi ne da zarar an ga wani mai ƙarzuwa a alumma, to wajibi ne a yi wa waɗanda ke kusa da shi ko muamula da shi magani irin wanda aka bai wa wanda ke da cutar.

Ya ce babu wani abu da za a ce mutum ya yi fiye da hakan, ba maganar a ƙara tsafta ba ne ko rigakafi.

Sai dai likitan ya ce bayan an bayar da maganin na sha ko na shafawa, kayyayakin da mutum ya sa a cikin kwanakin, ko zanin gado, sai an basu kulawa ta musamman kamar wanke su, da shanya su a cikin rana ko kuma goge su.

Ya kuma ce akwai buƙatar a tashi tsaye a wayar wa mutane kai kan cewa da an ga alamominsa a garzaya asibiti.

Farfesa Shehu ya ce cutar ta fi yaɗuwa a wurin da ke da taron mutane kamar gidajen yari, ko ɗakin almajirai, don haka akwai buƙatar mayar da hankali wuraren.