Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ƴanbindiga suka sace mutum 60 a Zamfara
Rahotonni daga jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na cewa ƴanbindiga sun yi garkuwa da mutum 60 a ƙauyen Sabon Garin Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura a ƙarshen mako.
Bayanai dai sun nuna cewa ƴanbindigar ɗauke da muggan makamai haye a kan babura sun yi wa ƙauyen ne shigar ba-zata ranar Asabar, kamar yadda Isa Sani wani mazaunin ƙauyen ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
"Da shigarsu ƙauyen ba su wata-wata ba sai suka fara da harbin kan mai-uwa-da-wabi inda kuma daga bisani suka yi garkuwa da mutum 60 da suka haɗa da ƙananan yara da ƴanmata. Kawo yanzu ba mu ji komai daga gare su ba. Ko'ina ya yi tsit." In ji Isa.
Sai dai mataimakin shugaban ƙaramar hukumar, Hon Mikaila Abba Bakura ya shaida wa BBC cewa mutane 20 aka sace.
Ƴanbindigar sun kuma kashe wani manomi sannan sun yi awon gaba ɗansa a wani ƙauye da ke maƙwabtaka mai suna Rogoji.
Wannan dai na zuwa ne ƙasa da mako guda bayan bayyanar wani bidiyo da ke nuna wasu gomman mutane da suka haɗa da maza da mata da kananan yara tare da ƴanbindiga.
Mutanen, waɗanda ake zargin cewa an sace su ne a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar, an nuna su ne suna zaune a wani wuri da ba a iya tantancewa ba, wasu daga cikinsu suna ɗaure da sarƙa.
Haka nan an rufe wa wasu daga cikin su fuskoki, inda aka ware mata da yara daban da maza.
Kayan da suke sanye da su sun nuna alamar jin jiki, yayin da mazan kuma suka yi gashi a fuska.
Ko a watan da ya gabata mai sai da ƴanbindigar suka yi wa wasu mutum 38 yankan rago a ƙauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda da jihar ta Zamfara.
Mutanen 38 na daga cikin mutum 5o da ƴanbindigar suka sace watanni huɗu kafin nan, kuma sun yi kisan ne sakamakon gaza biyan kuɗin fansa na mutanen 38.