Me ya sa Isra'ilawa ke son kawo ƙarshen yaƙin Gaza?

    • Marubuci, Lucy Williamson
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Middle East correspondent
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 7

A yayin da yaƙin Gaza ke shiga wata na 20, Amit Halevy ta yi ta maganganu cikin kururuwa, tare da jifa da duwatsu da kuma ƙwai a kan titunan Isra'ila, duk domin kiran dakatar da yaƙin Gaza.

''Za mu yi zaman dirshan mu yi shiru, wasu gungun mata ne kawai sanye da fararen kaya, riƙe da allunan da ke ɗauke da saƙonni cikin harsunan Hebrew da Larabci da kuma Turanci na cewa: 'tausayi', 'zaman lafiya', 'cikakken tsaro'," a cewarta.

"Muna tunanin: Waye zai ja da zaman lafiya? Amma wannan gangamin zai iya haifar da ƙiyayya, kamar lokacin da muka yi kiran dakatar da mamaya ko ƙyale Gaza.

Wani daga cikin masu zanga-zangar ya yi ta yin mana kururuwa a lokacin ganganimin zaman dirshan din da aka yi a Tel Aviv, inda ya ce ina ma ace duka an yi mana fyaɗe a Gaza, a lokacin da muke zaman dirshan ɗin riƙe da alluna masu ɗauke da saƙonnin ''Soyayya''.

Na fara haɗuwa da Amit a farkon watannin yaƙin. Jika da waɗanda suka tsira daga kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa (Holocaust) ta bayyana min yadda iyalai ke tattauna abin da ke faruwa a Gaza ke sanya ta fushi da damuwa. Ta yarda cewa abin da Isra'ila ke yi ya haifar da abin da sojojin Nazi suka yi.

A yanzu ta ce abubuwa na sauya a danginta.

"Mahaifina da kansa, ina faɗa masa abubuwan da bai saba ji ba'', in ji ta, amma yakan ce to Hamas ɗin fa? Amma sai na ce masa ''Baba idan har za a kashe yara 80 a dare guda, a ce ba za a ji wani abu ba? A matsayinmu na ɗan'adam, musamman Bayahude, ya kamata ka yi fatan dakatar da yaƙin yanzu'', kuma ya fahimceni.''

Adadin Isra'ilawan da ke ci gaba da nuna damuwa kan halin da Gaza ke ciki na ƙaruwa sannu a hankali, kuma Amit da ƙawayenta na ciki

Cibiyar Dimokaradiyya ta Isra'ila (IDI) ta tambayi 'yan ƙasar a watan da ya gabata ko wahalhalun da fararen hular Gazan ke ciki ya kamata ya zama abin la'akari kan matakan da gwamnati ke ɗauka kan yaƙin.

Mafi rinjaye - kashi 67 cikin 100 - sun ce ko dai Isra'ila ta yi watsi da shi ko kuma ta yi la'akari da shi. A tsakanin Yahudawa Isra'ilawa, wanda ya kai fiye da kashi uku cikin huɗu.

Yawancin Isra'ilawa, waɗanda suka ruɗe bayan yaƙin fiye da shekara ɗaya da rabi, yanzu suna son kawo ƙarshen yaƙin – mafi yawansu ba don wahalar da Gaza ke ciki ba, sai don Isra'ilawa 54 da ake garkuwa da su.

'Ana kange mutane daga abin da ke faruwa a Gaza'

An fara yaƙin ne bayan Hamas ta kai hari Isra'ila cikin watan Oktoban 2023, inda ta kashe mutum 1,200 tare da yin garkuwa da 251.

Tun daga lokacin aƙalla Falasɗinawa 54,607 aka kashe, a cewar ma'aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza. Majalisar Dinkin Duniya ta ƙiyasin cewa fiye da kashi ɗaya cikin huɗu na adadin ƙananan yara ne.

Bayan da Isra'ila ta wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Maris, wasu daga cikin ƙawayen Amit ƴan gwagwarmaya sun fara riƙe hotunan yaran da aka kashe da waɗanda aka jikkata a Gaza a lokacin zaman dirshan ɗin.

"Mun yi tunanin cewa za mu fuskanci suka da hamayya,' a cewar ɗaya daga cikin masu shirya zaman , Alma beck.

''Amma abin mamakin sai mutane suka riƙa tambayarmu, su wane ne waɗannan, me ya faru da su - Mutane sun riƙa ƙwaƙƙwafi saboda damuwa.''

Ta yi imanin cewa da dama cikin Isra'ilawa ba su da labarin uƙubar da ake ciki a Gaza.

"Gwamnati da kafofin yaɗa labarai, na yin komai don kange mutane daga sanin abin da ke faruwa a Gaza. Akwai katanga mai ƙarfi da ke hana mutane sanin abin da ke faruwa," in ji ta.

Ƙaruwar rashin gamsuwa da yaƙin

Masu zanga-zangar neman sakin waɗanda ake garkuwa da su da kuma ''dakatar da yaƙin'' riƙe da tuta mai launin bakan gizo na ci gaba da ƙaruwa a birnin Kudus a watan Yuni.

Yitzchak Zitter, mai neman jinsi tare da saurayinsa, da a yanzu haka ke cikin rundunar sojojin kota-kwana na Isra'ila, amma suke tunanin cewa bai kamata a ci gaba da yaƙin ba.

"Ba na tunanin mun kusa cimma ɗaya daga cikin muradun yaƙin da aka zayyna tun da farko," in ji shi.

"Shekara guda da ta gabata, bayyana irin wannan ra'ayi a bainar jama'a ba abu ne da ba a saba ji ba, musamman ga soja. Amma a yau mutane sun gaji da yaƙin, mun tsane shi, ya mun gaji. Kuma idan ka maido da mutanen da ake garkuwa da su, za a iya ƙara yarda da ra'ayin.

Maido da mutanen da Hamas ke garkuwa da su, shi ne babban dalilin da Isra'ilawa ke bayar wa na son kawo ƙarshen yaƙin.

Firaministan Isra'ila, Banjamin Netanyahu, na ci gaba da dagewa cewa ayyukan sojin ƙasar a Gaza na da matuƙar muhimmanci wajen sakin Isra'ilawan da suka rage a hannun Hammas.

Ya zuwa yanzu, sojojin Isra'ila sun kuɓutar da mutum takwas masu rai, yayin da aka saki fiye da 140 ta hanyar yarjejeniya da Hamas.

Netanyahu ya dage cewa matsin lambar sojojinsa ne ya tilasta Hamas amincewa da yarjejeniyoyin.

Amma da dama cikin masu zanga-zanga a wajen ofishinsa da ke birnin Ƙudus ko a Tel Aviv sun musanta hakan.

"Ba za mu iya maido da su a wannan siga ba," in ji ɗaya daga cikin masu zanga-zangar, wanda masanin halayyar ɗan'adam, Mayan Eliahu Ifhar. "Wannan babban kuskure ne. Yaƙin na kashe su."

Ana kuma ƙara nuna rashin jin daɗi kan ko za a iya cimma ɗaya burin na Mista Netanyahu a yakin, wato kawar da Hamas gaba ɗaya a matsayin rundunar soji da kuma jagorancin gwamnati.

'Yaƙin siyasa'

Bayan kusan wata 20, yaƙin na gimshi rundunar sojin Isra'ila.

Wannan ne yaƙin Isra'ila da aka jima ana fafatawa, kuma wasu daga cikin sojojin rundunar kota-kwana sun je fagen daga har sau wajen huɗu.

Amma bukatun kawo ƙarshen yaƙin - kama daga kan tituna, da wuraren ɗaukar sojoji, zuwa majalisar ministocinsa na tsaro - sun bar Netanyahu ba tare da sauya ra'ayinsa ba.

Wasu daga cikin dalilan da Farfesa Tamar Hermann na cibiyar IDI ke cewa mafi yawan masu kiran kawo ƙarshen yaƙin, mutane ne da suka ce ba za su sake zaɓarsa ba.

Fargabar mayaƙan Hamas su sake haɗuwa

Domin jin tunanin magoya bayan Netanyahu kan yaƙin, mun tuntuɓi masu gangamin goyon bayansa.

Na haɗu Yisrael da matarsa a kusa da ginin majalisar dokokin ƙasar, inda ya bayyana min ra'ayinsa.

"Ba za mu kawo ƙarshen yaƙin ba [yanzu," in ji Yisrael. "Za a kawo ƙarshensa ne a lokacin da aka kammala kakkaɓe Hamas da duka gine-ginenta, idan ka bar yaƙin yanzu za su sake gina komai, kuma yanayin zai sake dawowa cikin shekara uku zuwa huɗu.

Kamar sauran Isra'ila, ya amince cewa ƙwato waɗanda ake garkuwa da su na da matuƙar muhimmanci - amma ya ce akwai sauran abin ala'akari.

Haka shi ma wani mai zang-zangar goyon bayan yaƙin, Avigdor Bargil, ya ce za a kawo ƙarshen yaƙin ne kawai ''idan Hamas ta ajiye makamai ta miƙa wuya'' kuma dole Falasɗinawa su fice daga Gaza zuwa wasu ƙasashen irin su Indonesia da Faransa da Birtaniya.

"Saboda ba ƙasarsu ba ce , sun ƙwata ne,'' in ji shi. da na tambaye shi me ya sa ƴan Gaza za su fice daga ƙasarsu, sai ya ce ''wannan ƙasarmu ce, ƙasar da Ubangiji ya ba mu a cikin littafin Attaura."

Burin mamaye ƙasar Falasɗinu

Wannan dalili na addini da ake bayarwa na ƙwace ƙasar Falasɗinu ana yawan ambata ta bayan fara yaƙin, musamman a har a cikin jam'iyyun ƙawancen gwamnatin Netanyahu.

Ministocin gwamnatin, irinsu ministan kuɗi Bezalel Smotrich sun jima suna bayyana buƙatar ƙwace Gabar Yamma. Amma furucin Donald Trump na baya-bayan nan ya ƙara farfaɗo da wanann buri.

Kuma Netanyahu na buƙatar da ci gaba da ƙawancensa, ko kuma ya rasa kujerarsa, a cewar waa cibiyar binciken siyasa ta Amurka.

Bayan harin Hamas, tsohon rabuwar kawunan siyasar Isra'ila ta sake farfaɗowa.

Mayan Eliahu Ifhar, ƙwararriya kan ɗabi'ar ɗan'adam a Tel Aviv ta ce bambancin da yaƙin ya haifar sabani har ga ƙwayenta.

"A lokacin da na ji bom a Gaza, nakan ji ba daɗi, amma akwai ƙawayena da ke cewa Allah ya ƙara, don haka na daina zama tare da su, ba zan iya kallonsu da idona ba ."