Arsenal ta ragargaji Chelsea a kwantan Premier League

Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Arsenal ta sharara kwallo 5-0 a ragar Chelsea a kwantan wasan Premier League da suka buga ranar Talata a Emirates.

Minti hudu da fara wasa Gunners ta zura kwallo a ragar Chelsea ta hannun Leandro Trossard, kuma haka suka je hutun rabin lokaci.

Arsenal ta buga kwallo zuwa raga sau 13 tun kan hutu, karo na farko da ta yi wannan kwazon a wasa da Chelsea a Premier League, tun bayan 2003/04.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Arsenal ta kara na biyu ta hannun Ben White, sannan Kai Havertz ya ci biyu a fafatawar ta hamayya.

Kenan Havert ya zama na farko da ya ci Chelsea kwallo biyu a Premier League, bayan da ya buga wa kungiyar Stamford Bridge tamaula a baya.

Wannan shi ne karon farko da Arsenal ta dura 5-0 a ragar Chelsea a gida a babbar gasar tamaula ta Ingila, tun bayan 5-2 da ta yi nasara ranar 16 ga watan Afirilun 1979 lokacin rukunin farko

Daga karshe Ben White ne ya zura na biyar a ragar Chelsea, saura minti 20 a tashi daga wasan.

Chelsea ta fara karawar da 'yan wasa masu matsakaicin shekara kasa da 24, kuma a karo na bakwai da ta yi hakan a Premier League a bana.

Leeds United ce kan gaba a irin wannan kokarin a 1999/2000, wadda ta yi hakan karo 10.

Mauricio Pochettino

Asalin hoton, Getty Images

Da wannan sakamakon Arsenal tana ta daya a kan teburi da maki 77, sai Liverpool ta biyu da maki 74 da kuma Manchester City mai maki 73 mai kwantai biyu.

Chelsea kuwa tana ta taran teburi da maki 47 da tazarar maki daya tsakani da West Ham ta takwas da tazarar maki uku tsakani da Manchester United ta bakwai da Newcastle United ta shida masu maki 50 kowacce.

Ranar Lahadi 28 ga watan Afirilu Arsenal za ta je gidan Tottenham a wasan mako na 35, shima wasan hamayya.

Ita kuwa Chelsea mai kwantan wasa biyu, za ta je gidan Aston Villa ranar Asabar 27 ga watan Afirilu.