Rayuwa ta fara komawa yadda take a Tundun Biri

Tudun Biri

Asalin hoton, Nigerian Army

An wallafa

Al’amura sun fara komawa kamar yadda suke a baya, a kauyen Tudun Biri da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, bayan mutuwar mutum fiye da 100 a wani hari da jirgin soji marar matuki ya kai kan masu taron Mauludi a watan da ya gabata.

Kawo yanzu dai an sallami da dama daga cikin mutanen da aka kwantar a asibiti sakamakon raunuka da suka ji a lokacin harin.

Wakilin BBC da ya ziyarci yankin ya yi bayanin cewa abin farko da ake fara gani idan aka tunkari ƙauyen shi ne hanyar da aka fara yi da za ta kai cikin garin.

A cewar wasu mazauna yankin rayuwarsu ta fara komawa kamar yadda take a baya kafin aukuwar harin.

Ɗaya daga cikin dattawan garin, Mallam Suleiman Umar ya ce ya fara samun daidaituwa a al'amuransa bayan ya shafe kwana 23 yana jinya a asibiti sakamakon harin.

'Jiki yanzu Alhamdulillahi, har ma na je na dubi gonata, kuma komai yana nan yadda na bar shi, ana kuma ci gaba da noma' in ji shi.

Ya ƙara da cewa yanzu an sami cigaba a garin sakamakon abubuwan more rayuwa da gwamnatin ta yi alƙawarin kawowa ga mutanen yankin.

Baya ga alƙawuran da hukumomi suka yi, a halin yanzu an fara shirin gina wani katafaren masallacin Juma'a wanda wani ya ɗauki nauyin ginawa al'ummar yankin.

Shugaban kwamitin harkokin addinin Muslunci a majalisar dokokin jihar Kaduna, Mohammed Jamilu Albani ya bayyana cewa cigaban da yankin ke samu yanzu na cikin alherin da ya biyo bayan jarrabawar da ta faɗa wa yankin na harin da aka kai wa masu taron maulidi.

Ya ce ''wannan masallci zai ɗauki aƙalla mutum 2300 zuwa 2500, saboda haka wannan a wajenmu rana ce mai cike da tarihi.''

Ya bayyana ginin masallacin juma'ar a matsayin babban abin alheri wanda kuma zai taimaka wurin farfaɗo da al'amuran mutanen yankin.

Rahotanni da aka samu sun ce gwamnatin jihar Kaduna ta ƙaddamar da wani kwamiti na musamman da zai tattara bayanai da kuma kuɗaɗen da aka samu daga hukumomi da kuma ɗaukacin al'umma da nufin tabbatar da cewa al'ummar ƙauyen sun amfana kai-tsaye.