Arsenal za ta ziyarci West Ham ranar Lahadi a Premier League

Premier League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

West Ham United za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na 24 a gasar Premier League ranar Lahadi.

Arsenal tana ta ukun teburi da maki 49, ita kuwa West Ham mai maki 36 tana ta bakwai a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan wasa 23 kowacce.

Wannan shi ne wasa na uku da za su kara a tsakaninsu a bana, inda West Ham ta fitar da Gunners da cin 3-1 a League Cup ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba.

Sannan West Ham ta je ta ci Arsenal 2-0 ranar 28 ga watan Disamba a wasan farko a Premier League na kakar nan da suka kece raini a Emirates.

Sai ɗan wasan West Ham, Lucas Paqueta ba zai buga karawar ba, har yanzu Michail Antonio yana jinyar raunin gwiwa.

Arsenal tana da tabbaci Bukayo Saka zai iya murmurewa ya buga mata wasan na hamayya, wanda aka ga ya dingisa a karawa da Liverpool.

Oleksandr Zinchenko da Gabriel Jesus na jinya, wadanda za a auna koshin lafiyarsu, kafin wasan na ranar Lahadi.

KARAWA TSAKANIN KUNGIYOYIN BIYU

West Ham na fatan cin Arsenal gida da waje a lik a bana a karon farko tun bayan 2006-07.

Rabonda West Ham ta yi nasara a kan Gunners sau uku a jere tun bayan 1924-25.

Wasa daya aka ci Arsenal daga 15 baya a Premier League a waje da ta kara da West Ham da cin tara da canjaras biyar.

WEST HAM UNITED

David Moyes

Asalin hoton, Getty Images

Rashin nasara da West Ham ta yi a Manchester United a makon jiya, ya kawo karshen fafatawa shida ba tare da an doke ta ba, wadda ta ci uku da canjaras uku.

Tana bukatar nasara daya ta yi kan-kan-kan da tarihin yawan lashe wasa 11 kamar yadda ta yi a Premier League a bara.

Tun daga karshen Oktobar 2023, har yanzu ba a ci West Ham ba a gida, wadda ta yi nasara shida da canjaras hudu.

To amma har yanzu ba ta ci wa a 2024 ba, wadda ta yi canjaras hudu aka doke ta biyu, watakila ta kasa yin nasara karo na biyar da shiga sabuwar shekara tun bayan 1997.

Jarrod Bowen na bukatar cin ƙwallo daya a raga ya zama iri daya da yawan wadanda ya ci a bara. Ya kuma ci Arsenal a dukkan karawa hudun da ya yi da ita a dukkan fafatawa.

ARSENAL

Mikel Arteta

Asalin hoton, Getty Images

Arsenal na fatan cin wasa na hudu da fara sabuwar shekara a lik, karon farko tun bayan 1935.

Wasa daya Gunners ta yi nasara daga hudu baya a waje a Premier League mai canjaras daya da rashin nasara biyu.

Ƙwallo 11 ne ya shiga ragar kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama a Premier, ita ce mai ƙarancin ƙwallaye da aka ci a waje a bana.

To sai dai wasa daya ne ta buga da ƙwallo bai shiga ragar Arsenal ba daga 12 da ta je waje a dukkan fafatawa kawo yanzu.

Arsenal ta barar da maki daga wasa biyar a cikin bakwai a Premier League a wasan hamayya da ƙungiyoyin Landon.

Haka kuma Gunners ta ci kwallo takwas a Premier League ana daf da tashi a bana, wadda ba a yi wa haka ba a wasannin da take yi kawo yanzu.