Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu biyar da Bayern ke gaban PSG a Champions League
Paris St Germain ta ziyarci Bayern Munich, domin buga wasa na biyu zagayen 'yan 16 a Champions League ranar Laraba.
Bayern ce ta yi nasara a karawar farko da ci 1-0 a Faransa da suka fafata ranar 14 ga watan Fabrairu.
Wasa na 13 da za su kece raini tsakaninsu a wasannin Zakarun Turai, inda kowacce ta ci shida-shida.
Abubuwa biyar da Bayern Munich ta sha gaban Paris Saint-Germain
1. Bayern tana da Champions League shida
Bayern tana da Champions League shida jimilla, ita kuwa PSG har yanzu na fata, kungiyar Jamus ta doke ta Faransa 1-0 a wasan karshe a kakar 2020.
Da yake Bayern ce ta ci wasan farko a bana, karo 22 da ta yi haka ta kai zagayen gaba, in banda biyu da aka yi waje da ita.
A kuma karawa 10 da ta yi gasar Zakarun Turai, sau daya aka fitar da ita a 2010/10, wadda ita ce ta fara cin wasa a zagayen ziri daya kwale.
2. Bayern tana da 'yan bayan da ke hana kwallo shiga raga
Kwallo bai shiga ragar Bayern ba a wasa shida daga bakwai da ta kara a kakar nan a Champions League.
Kungiyar Jamus tana cikin 'yan biyar din da suka yi wasa shida kwallo bai shiga ragarsu ba, hudu daga ciki sai da suka kai karawar karshe a Champions League.
3. Kakar bana iri daya ce da wadda Bayern ta ci kofi uku a 2019/20
Da yake Bayern ta yi nasara a karawa bakwai a Champions League a kakar nan, irin hakan ta taba yi a 2019,20, wadda ta dauki kofi uku a lokacin.
4. Filin Allianz Arena ya zama kalubale ga kungiyoyin da suka kai ziyara
Ba a doke Bayern ba a gida a karawa takwas baya a Champions League.
Kungiyar Jamus ta yi nasara a fafatawa 15 daga 17 a gida a Champions League da canjaras daya aka doke ta wasa daya.
Wasa daya da aka doke ta shine 3-2 da PSG ta ci a quarter finals a 2020/21.
5. Nasarar Bayern a Faransa kan iya ba ta damar kai wa zagayen gaba
Wannan shi ne karo na 13 da za su fuskanci juna a tsakaninsu, kowacce ta ci shida-shida, sai da Bayern ta yi nasara a wasa biyar daga bakwai baya.
Haka kuma Bayern ta ci fafatawa uku daga hudu baya da ta yi a gida da PSG.