'Ina jin da ma Allah bai halicci mata ba'

An wallafa

Wata Budurwa mai shekara 19 da manufofin gwamnatin Afghanistan suka daƙile wa burinta na zuwa jami'a a ƙasar, ta ce takurawar da ake yi wa mata a Afghanistan ko dabbobi ba a yi wa ita".

Watanni kaɗan suka rage mata ta zama mace ta farko a cikin danginta da za ta fara zuwa jami'a amma sai ga shi Taliban ta hana ta damar samun karatun jami'a da kuma yin aiki da ƙungiyoyin ba da agaji a makon da ya gabata.

"Dabbobi za su iya zuwa ko'ina, amma mata ba su da ƴancin yin hakan, ko da kuwa fita daga gidajensu ne" a cewar ta."

"Ji nake da ma Allah bai halicci mata ba. Idan har za mu zama marasa sa'a haka, gara ma a ce ba a halicce mu ba tun farko.'

Ta ce "ana ɗaukar mu ƙasƙantattun fiye ma da dabbobi, domin dabbobi za su iya zuwa duk inda suke so, amma 'yan mata ba sa iya fita ko nan da ƙofar gida."

A makon jiya ne gwamnatin Taliban ta haramta wa mata damar karatu a jami'o'i da kuma aiki da ƙungiyoyin ba da agaji.

Abin da MDD ta ce game da matakin Taliban

Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi tur da manufofin Taliban a kan 'yan mata da mata a ƙasar ta Afghanistan.

Kwamitin mai wakilcin ƙasashe 15 ya ce ya damu matuƙa game da ƙarin takunkuman da Taliban ke ƙaƙabawa a kan ilimin 'ya'ya mata.

Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres ya ce ya zama wajibi a soke waɗannan matakai na baya-bayan nan.

A wata sanarwar da ta fitar, MDD ta buƙaci a bai wa 'yan mata da mata damar shiga a dama da su cikin duk wasu harkoki na tafi da ƙasar.

Sanarwar ta buƙaci Taliban ta buɗe makarantu sannan ta gaggauta soke matakan tauye rayuwar mata, waɗanda ta ce suna nuna yadda ake samu raunin martaba ƴancin ɗan'adam a Afghanistan.

A baya-bayan nan ma, Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ta dakatar da wasu aikace-aikace masu matuƙar muhimmanci na gaggawa saboda hana matan ƙasar aiki da ƙungiyoyin ba da agaji da gwamnatin Taliban ta yi.

Majalisar Duniya ta ce mai yiwuwa ne sauran aikace-aikace da yawa ma za a buƙaci dakatar da su, yayin da take nanata kira ga Taliban ta warware shawarar da ta ɗauka.

A cikin wata sanarwar haɗin gwiwa, Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu manyan ƙungiyoyin ba da agaji masu yawa sun ce shigar da mata cikin ayyukan ba da agaji ba batu ne na tattaunawa ba, don haka dole sai da su aiki zai ci gaba.

Ba dukkan ma'aikatun gwamnatin Taliban ne ke goyon bayan matakin hana mata aiki da ƙungiyoyin ba da agajin ba.

Babban jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya kan ayyukan jin ƙayi na haɗin gwiwa ya ce ma'aikatar lafiya ta yarda cewa ya kamata mata su ci gaba da ayyukan da suka shafi kula da lafiya.

Sauran ma'aikatun kuma an ba da rahoton cewa suna tuntuɓar Majalisar Ɗinkin Duniya inda suke cewa kamata ya yi a bar mata su yi aiki da hukumomin kai ɗaukin gaggawa da tunkarar bala'o'i.