Jiragen ruwa 50 na jiran izinin wucewa ta Hormuz
Hukumar Rediyo da Talabijin ta Iran ta ce “kimanin jiragen ruwa 50” ne ke jiran a mashigar Hormuz domin rundunar sojin ruwa ta Juyin Juya Hali ta ba su izinin wucewa.
Wannan na zuwa ne yayin da Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Tekun Farsi ta sanar a ranar Alhamis cewa an rufe mashigar ga jiragen kasuwanci da tankokin mai har sai an sake bayar da wata sanarwa, sakamakon tashin hankalin da ke tsakaninta da Amurka.
Hukumar ta kuma bayyana cewa jiragen da suka samu “izinin wucewa” su ci gaba da jiran ƙarin umarni.
“Yankin yammacin mashigar Hormuz, mashigar kanta, da kuma Tekun Farsi na karkashin cikakken ikon rundunar sojin ruwa ta IRGC, yayin da gabashin mashigar Hormuz da arewacin Tekun Indiya ke karkashin ikon rundunar sojin ruwa ta sojin ƙasa. Babu wani jirgin ruwa da zai iya shiga wannan mashiga ba tare da izininmu ba," in ji Habibollah Sayyari, Babban Hafsan Sojin Iran kuma mataimakin mai kula da rundunar.