Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ba na son duba madubi saboda yadda na sauya daga zankaɗeɗiyar budurwa zuwa wata halitta'
A lokacin da aka haifi Violet, ba ta da wata nakasa kuma a lokacin da take tasowa, ta fara girma ne kamar yadda take son zama.
Wannan shi ne dalilin da ya sa ta kaɗuwa tare da ɗimuwa a lokacin da kwatsam rayuwa ta sauya a gare ta.
Binciken likitoci ne ya gano cewa Violet 'yar shekara 27 tana ɗauke da wata baƙuwar cuta mai suna Sclerodema da ba ta magani.
Cuta ce mai matuƙar wahala wadda ba kasafai ake samun irinta ba, cuta ce da ke sanya fata ta yi tauri kuma ta motse.
Haka zalika, cutar ta fi kama mata a kan maza, duk da yake ba a warkewa amma akwai magungunan rage kaifi cutar da dakushe ƙarfinta.
Yadda cutar ta faro
Violet, 'yar asalin jihar Delta a kudu maso kudancin Najeriya ta shaida wa BBC yadda cutar ta canza mata rayuwa. Matashiyar ta ce bayan kammala karatun diploma a jihar tana cikin tunanin fara aiki ne a lokacin da rayuwa ta yi mata tutsu.
Ta ce da farko, wani ɗigon baƙi ne ya fara fito mata a gadon baya, sai kuma ya bayyana a hannayenta, daga nan sai hannuwan suka yi baƙi ƙirin.
Wannan shi ne farkon wannan cuta maras magani da Violet ke fama da ita kamar yadda ta shaida wa BBC. A yayin da cutar ta ci gaba da yaɗuwa a jikinta, sai kamanninta suka fara canzawa zuwa wata irin halitta, da ko ita ma ba ta son ganin kanta. ''ina cikin damuwa saboda canzawar kamanni da na samu'' in ji ta.
''Ko madubi a wasu lokuta ba na son kalla, saboda sai na ji a raina cewa wai kyakkyawar yarinya kamata ni ce na koma wata iri daban, amma daga baya sai na saduda na karɓi ƙaddarata'' in ji Violet wadda ta ce ko ƙofar gida ba ta iya fita.
Ta kara da cewa ''Babu inda nake zuwa, kullum ina gida, ba labarin ci gaba da karatu, gaskiya ina cikin matsananciyar damuwa game da halin da nake ciki''
'Likita ya ce cutar ba ta da magani, amma na yi imani zan warke wata rana'
Violet da iyayenta sun yi ta zirga-zirgar neman magani a wurare daban-daban cike da fatan samun waraka, amma har yanzu haƙarsu ba ta cimma ruwa ba. Kama daga asibitoci zuwa masu maganin gargajiya, babu wanda ya ce musu ga ainihin abin da yake damun ta, babu kuma wani haske game da warakarta.
''Mun je wurare da dama domin neman magani. mun je asibitoci masu yawa, kuma duk asibitin da muka je sai su ce mana ba su ga komai ba, haka su ma masu maganin gargajiya, wasunsu sai su ce rauni ne, wasu kuma su ce guba na ci, wasu ma su ce tsafi ne, da dai abubuwa masu yawa'' kamar yadda ta bayyana.
Bayan zuwa wuraren neman magani da dama, a halin yanzu Violet na karɓar magani a asibitin jihar Delta inda take ƙarƙashin kulawar likitan fata.
Duk da yake, likitan ya shaida wa Violet tare da iyayenta cewa cutar da take ɗauke da ita ba ta da magani, har yanzu tana cike da fatan cewa wata rana za ta warke.
''Likita ya ce cutata ba ta da magani, amma ni ban yarda cewa ba zan warke ba, don kuwa na yi amanna cewa wata rana zan warke'' kamar yadda Violet ta shaida wa BBC cike da ƙwarin gwiwa.
'Iyayena sun yi min komai'
A yayin da take bayyana yadda take fama da cutarta musamman yadda al'umma ke kallon ta, Violet ta yaba wa iyayenta saboda yadda suke ba ta kulawa. Ta ce da a ce ba ta samun kulawar iyaye, da komai ya sukurkurce mata.
'Iyayena sun zame min komai a rayuwata. musamman mahaifina da mahaifiyata. Allah ne kawai zai biya su abin da suka yi min''.
Ta ce tana iya tuna yadda take da ƙawaye da abokai masu yawa kafin ta gamu da lalurar, amma yanzu da dama sun juya mata baya.
'Mutane na cewa ina burge su'
Ta ce mutane da dama na amfani da shafinta na TikTok suna ƙarfafa mata gwiwa. Duk da yake wasu mutane a dandalin na yi mata shaguɓe da ba'a, akwai wasu da ke furta mata kalaman soyayya da ƙarfafa gwiwa.
''Mabiyana a shafin da yawa na yi mini ba'a, a yayin da wasu daga cikinsu ke cewa suna sona tare da alkawarin nuna min soyayya da kulawa''
"A wannan dandali na ga mutanen da na iya cewa suna nuna min soyayya tamkar 'yan uwana," in ji matashiyar. "Wasu mutane da dama na zuwa shafina su ce min ina ƙarfafa zukatan jama'a. Wasu ma har tambaya ta suke yi 'shin mene ne sirrin ƙarfin halin rayuwata duk da haka kwatsam larura ta zo ta sa ba kya iya tashi tsaye har ki yi tafiya, amma yanzu kina iya tattakawa'".
Jin cewa ina ƙarfafa zukatansu ya sa ni yin godiya ga Allah da ya sanya duk da halin da nake ciki amma na zama mai sanya haske a zukatan wasu," ta ƙara da cewa.
Me muka sani game da cutar yanƙwanewa da taurin fata?
Cutar yanƙwanewa da taurin fata wato Scleroderma a Turance rukunin wasu baƙin cutuka ne da ke sanya fatar jiki ta yi tauri kuma ta tattare.
Suna kuma iya janyo matsaloli ga jijiyoyin jini da sassan cikin jiki da tumbin mutum. cutar taurarewar fata akasari ana kasa ta zuwa "taƙaitacciya" ko "mai mamaye jiki," don haka ya danganta da yawan sashen jiki da cutar ta karaɗe.
Duk nau'o'in biyu suna iya haddasa matsaloli ga jijiyoyin jini da gaɓoɓin jiki. Cutar taurarewar fata da ke kama wani sashen jiki ta fi shafar fatar ce kawai.
Duk da yake ba a san maganin cutar taurarewar fata ba, ƙwararru sun ce akwai magungunan rage kaifin cutar, da dakushe ƙarfinta, kuma suna iya inganta matsayin rayuwar mai fama da ita.
Kowanne jinsi na iya kamuwa da cutar taurarewar fata, amma dai ta fi faruwa a kan mata idan an kwatanta da maza. Ɗumbin sabubba ne ga alama suke janyo kasadar samun cutar.