Za a yi karon batta tsakanin Barca da Atletico ranar Lahadi

An wallafa

Barcelona za ta karbi bakuncin Atletico Madrid ranar Lahadi a wasan mako na 15 a La Liga, karawar hamayya.

Kungiyoyin biyu sun kara a bara a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, inda Barcelona ta yi nasara gida da waje.

Kakar 2022/2023

Sifanish La Liga Lahadi 23 ga watan Afirilun 2023

  • Barcelona 1 - 0 Atl Madrid

Sifanish La Liga Lahadi 8 ga watan Janairun 2023

  • Atl Madrid 0 - 1 Barcelona

Kawo yanzu Real Madrid ce ta daya a kan teburi da maki 35, iri daya da na Girona ta biyu.

Ranar Asabar Real Madrid na karbar bakuncin Granada, a kuma ranar Valencia za ta ziyarci Girona a dai karawar ta mako na 15 a La Liga.

Atletico ce ta uku mai maki 31. iri daya da wanda Barcelona take da shi, bayan kammala karawar mako na 14.

Barcelona ta ci karo da koma baya a La Liga karawar mako na 14 ranar 25 ga watan Nuwamba, inda ta tashi 1-1 a gidan Rayo Vallecano.

To sai kungiyar da Xavi ke jan ragama ta doke Porto a Champions League 2-1 ta koma jan ragamar teburi, saura wasa daya ya rage musu.