Bikin Ranar Mata a Fannin Kimiyya ta Duniya 2023

Bayanan bidiyo, Latsa wannan hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Bikin Ranar Mata a Fannin Kimiyya ta Duniya 2023
An wallafa

Akwai wagegen giɓi tsakanin ɗalibai maza da mata a dukkan fannoni na kimiyya da fasaha har ma da lisafi a dukkan sassan duniya.

Amma duk da cewa mata sun sami gagarumin ci-gaba a fagen shiga cikin masu ilimin gaba da na sakandare, har zuwa yau akwai bukatar shigar da karin mata masu yawa a wadannan fannonin.

A ranar 20 ga watan Disambar 2013, babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kuduri na ba mata damar samun daidaito da maza a dukkan fannoni na kimiyya da fasaha, inda ya ce wannan matakin zai taimaka wajen 'yantar da mata da 'yan mata.

A kan haka ne BBC ta tattauna da Maryam Umar Mairiga, wata daliba da ke aji na uku a babbar sakandire mai koyon kimiyya a Najeriya.