Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United za ta fuskanci Arsenal da Liverpool da Betis a Amurka
Manchester United za ta ci gaba da buga wasannin sada zumunta a Amurka, domin shirye-shiryen tunkarar kakar 2024/25.
Ranar Asabar ƙungiyar Old Trafford ta doke Rangers 2-0 a Edinburg, wasa na biyu kenan da ta yi bayan rashin nasara a hannun Rosenborg a watan Yuli.
Ƙungiyar da Erik ten Hag ke jan ragama za ta fafata da Arsenal a Los Angeles da fuskantar Real Betis a San Diego da kuma Liverpool a Kudancin Carolina.
Marcus Rashford da Harry Maguire da kuma Antony ba su buga wasan da United ta ci Rangers ba, amma za ta je da su Amurka, domin wasannin sada zumuntar.
Sabon ɗan wasan da United ta ɗauka a bana, Leno Yoro ya buga karawar da aka yi a Murrayfield Stadium, wanda zai bi ƙungiyar zuwa Amurka..
Wasannin United da za ta buga a Amurka
Arsenal - 27 ga watan Yuli
A filin wasa na SoFi Stadium a Los Angeles
Real Betis - 31 ga watan Yuli
A filin wasa na Snapdragon Stadium a San Diego
Liverpool - 3 ga watan Agusta
A filin wasa na Williams-Brice Stadium a Kudancin Carolina
Manchester United ta kare a mataki na takwas a Premier League da aka kare da maki 60, bayan karawa 38.
Haka kuma an fitar da ita a cikin rukuni a Champions League, yayin da Newcastle United ta yi waje da ita a League Cup, wanda take rike da kofin a bara.
To sai dai United ta samu gurbin shiga gasar Europa League ta bana, bayan da ta ci Manchester City ta kuma lashe FA Cup a cikin watan Mayu.