Man Utd na zawarcin Mateta, Chelsea ta matsa ƙaimi kan Rodriguez

Jean-Philippe Mateta

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United na duba yiwuwar saye ɗan wasan gaba a Crystal Palace da Faransa, Jean-Philippe Mateta mai shekara 27. (Sun - subscription required)

Real Madrid da Bayern Munich da Chelsea da kuma Tottenham sun shiga zawarcin ɗan wasan Bournemouth da Sifaniya mai shekara 19, Dean Huijsen da ake son sayarwa kan fam miliyan 50. (Mail - subscription required)

West Ham da Crystal Palace na cikin ƙungiyoyin da ke son saye ɗan wasan Southampton da Ingila, Taylor Harwood-Bellis mai shekara 23 a wannan kaka. (Football Insider)

Atletico Madrid na shirin gabatar da tayin fam miliyan 50 kan ɗan wasan Marseille da Ingila, Mason Greenwood mai shekara 23 a karshen kaka. (Fichajes - in Spanish)

Ɗan wasan tsakiya a Jamus, Joshua Kimmich mai shekara 30, na son tafiya Bayern Munich a wannan kaka duk da tayin da ya ke samu daga Arsenal da Paris St-Germain. (Sky Germany)

Chelsea na son ɗan wasan Sifaniya da Real Betis, Jesus Rodriguez mai shekara 19, da ke iya tafiya kan fam miliyan 42, kuma Liverpool ita ma na bibiyarsa. (Mail)

Manchester United da Liverpool sun tuntubi Atalanta kan ɗan wasan tsakiyarta daga Brazil, Ederson duk da cewa Manchester City ita ma ta nuna kwaɗayinta kan matashin mai shekara 25 da aka yi wa kuɗi fam miliyan 50. (Caught Offside)

Manchester United na fatan ciniki a lokacin bazara kafin kaddamar da burinta na neman saye ɗan wasan RB Leipzig da Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 21 kan yuro miliyan 80. (Caught Offside)

Liverpool ita ma na son Sesko ya kasance cikin 'yanwasan da za ta siyo domin garambawul a ƙungiyar. (Give Me Sport)

Liverpool na duba yiwuwar ba da aro ɗan wasanta mai shekara 21 Harvey Elliott, a sabuwar kaka. (Football Insider)

Barcelona na ba da fifiko wajen sabunta yarjejeniya da ɗan wasan tsakiya a Netherlands, Frenkie de Jong mai shekara 27, bayan Arsenal tayi kokarin soma harinsa. (Sport - in Spanish)