Man United ta doke Plzen da gumin goshi

A

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United ta samu nasarar doke Viktoria Plzen har gida da gumin goshi a gasar Europa.

Da wannan sakamakon ƙungiyar ta Ruben Amorim ta koma cikin jerin ƙungiyoyin takwas ɗin farko da ba za su yi neman gurbi ba a gasar.

A minti na 48 da fara wasan ne golan United Onana ya tafka kuskure da ya kai ga bai wa ɗan wasan gaban Plzen Matej Vydra damar jefa kwallo ta farko a ragar a wasan.

Bayan sauya Rashford da ya yi Rasmus Hojlund ya farke wa ƙungiyar kwallon da aka zura mata a mintina na 62 bayan dawowa hutun rabin lokaci kenan.

A minti na 88 Bruno Fernandes ya ƙara bai wa Hojlund dama ta sake zura kwallo a raga a daf da tashi daga wasa.

Da haka aka tashi daga wasan Manchester United ta haɗa maki uku amma da jiɓin goshi.

Yanzu Hojlund ya ci kwallo biyar kenan a wannan gasa, kuma da haka Manchester ta koma ta takwas a teburi.

United na fama da rashin tabbas kan wadanda za su riƙa buga mata wasa a kullum, wani abu da ake kallo a matsayin gyara da Amorim ke neman kawo ƙungiyar.