Napoli ta ɓarar da damar komawa kan teburin Serie A

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Napoli ta ɓarar da damar komawa kan teburin Serie A, sakamakon rashin nasara a hannun Como da ci 2-1 ranar Lahadi a Stadio Giuseppe Sinigaglia.

Karon farko da aka ci Napoli daga wasa 11 a Serie A na bana, kuma ta ci gaba da zama ta biyu a kan teburi da maki 56, bayan wasan mako na 26.

Kenan da tazarar maki ɗaya tsakani da Inter Milan mai jan ragamar teburin babbar gasar tamula ta Italiya. Ita kuwa Como tana ta 13 da maki 28.

Como ta fara nasara ne sakamakon da Amir Rrahmani ya ci gida a minti na bakwai da fara wasan.

Sai dai minti 10 tsakani Napoli ta farke ta hannun Giacomo Raspadori, haka suka je hutu wasan yana 1-1.

Saura minti 13 a tashi daga karawar mai masaukin ɓaki ta kara na biyu ta hannun Assane Diao, kuma na uku da matashin mai shekara 19 ya zura a raga a Serie A.

Duk da cin gida da Napoli ta yi a wasan ita ce ta rike kaso mafi tsoka a fafatawar da kaso 60 cikin 100 tun kan hutu.

A zagaye na biyu ne Como ta karɓe ragama wasan, wadda karo na biyu da ta ci Napoli kenan tun bayan 1952 a Serie A.

Wasan gaba na Napoli shi ne za ta karɓi bakuncin Inter Milan, wadda ta yi nasara a kan Genoa 1-0 ranar Asabar.