Premier: Ƴan wasan da aka dakatar saboda karɓar katin gargadi biyar

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Katin gargadi yana ɗaya daga cikin abinda ke hana ɗan wasa taka leda a Premier League da zarar ya karɓi biyar jimilla.

Ranar Asabar za a ci gaba da zagaye na 20 a babbar gasar tamaula ta Ingila, inda ƴan wasa huɗu ba za su buga karawar ba, sakamakon kati mai ruwan ɗorawa biyar da aka yi musu.

Ƴan wasan sun haɗa da na Aston Villa, Morgan Rogers, wanda ya karbi kati mai ruwan ɗorawa a wasa da Brighton da na Newcastle United, Fabian Schar a karawa da Manchester United.

An bai wa ɗan wasan Southampton, Mateus Fernandes kati mai ruwan ɗorawa a wasa da Crystal Palace da na Tottenham, Rodrigo Bentancur, wanda ya kammala dakatarwa wasa bakwai, ya karɓi katin gargadi a wasa da Wolverhampton.

Kenan dukkansu huɗun ba za su kara a wasannin mako na 20 ba.

Wasannin mako na 20 a Premier League:

Ranar Asabar 4 ga watan Janairu

  • Tottenhamda Newcastle United
  • Bournemouthda Everton
  • Aston Villa da Leicester City
  • Crystal Palaceda Chelsea
  • Manchester City da West Ham United
  • Southampton da Brentford
  • Brighton da Arsenal

Ranar Lahadi 5 ga watan Janairu

  • Fulham da Ipswich Town
  • Liverpoolda Manchester United

Tuni Matheus Cunha ya fara hutun wasa biyu, bayan rashin da'a a wasan da Wolverhampton ta yi da Ipswich Town zagaye na 16.

To sai wasa ɗaya ne Cunha ba zai yi ba a Premier League, bayan da ɗayan ya shafi FA Cup zagaye na uku.

Kenan ɗan wasan tawagar Brazil zai iya buga wa Wolverhampton wasan mako na 21 da za ta kara da Newcastle United.

Haka shima Jhon Duran ya fara hutu daga dakatarwa uku, bayan rashin da'a da ya yi a wasan da Newcastle ta doke Aston Villa 3-0 a Premier League.

Kenan ba zai buga gasar Premier League ɗaya ba da FA Cup zagaye na uku da za ta fafata da West Ham United.

Ƴan wasa 11 da suka kammala hukuncin dakatarwa, kafin mako na 20 a Premier League:

Yan wasan West Ham United, Tomas Soucek da Guido Rodriguez da na Nottingham Fores, Ryan Yates da na Bournemouth, Justin Kluivert da na Crystal Palace, Marc Guehi da na Liverpool, Dominik Szoboszlai da kuma na Leicester City, Jordan Ayew.

Bruno Fernandes da Manuel Ugarte za su iya buga wa Manchester United Utd wasan da za ta je Liverpool, bayan dakatar da su.

Hak shima ɗan wasan Tottenham, Djed Spence da na Aston Villa, Matty Cash za su iya buga karawar mako na 20 a babbar gasar tamaula ta Ingila.