Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta ragargaji Salzburg a Champions League
Real Madrid ta faɗaɗa damar kare kofin Champions League a bana, bayan doke Red Bull Salzburg 5-1 a wasa na bakwai a cikin rukuni ranar Laraba.
Tun farko an doke Real karo uku daga wasa shidan farko, wannan nasarar da ta doke ƙungiyar Austalia, ya kara mata karfin gwiwa a gasar ta zakarun Turai ta bana.
Cikin waɗanda suka ci mata ƙwallayen sun hada da Kylian Mbappe da kuma Rodrygo da Vinícius Júnior da kowanne ya zura biyu a raga.
Ita kuwa Red Bull Salzburg ta zare ɗaya ta hannun Bidstrup, saura minti biyar a tashi karawar.
Da wannan sakamakon Real Madrid tana ta 16, jerin cikin waɗanda za su buga karawar cike gurbi a kakar bana da maki 12.
Ita kuwa Salzburg mai maki uku tana ta 34 daga wasannin ƙungiya 36, kenan za ta yi ban kwana da gasar zakarun Turai ta bana.
Yanzu saura karawa ɗaya ta rage a cikin rukuni, inda ranar Laraba 29 ga watan Janairu Real Madrid za ta je Brest.