Arsenal ta amince ta ɗauki Merino daga Real Sociedad

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta amince za ta biya 32.67m kuɗin sayen ɗan ƙwallon tawagar Sifaniya, Mikel Merino daga Real Sociedad.

Tun farko kuɗin ɗan ƙwallon ya kai £28.43m, sai kuma karin tsarabe-tsarabe da ya kai £4.24m..

Merino yana cikin tawagar Sifaniya da ta lashe Euro 2024 a Jamus, ya kuma buga dukkan wasa bakwai da cin Jamus ƙwallo a zagayen kwata fainal.

Mai shekara 28 yana da sauran ƙunshin kwantiragin da bai kai kaka daya ba a Real Sociedad mai buga La Liga.

Merino shi ne na uku da Gunners ta ɗauka a bana, bayan ɗan kasar Italiya, Riccardo Calafiori da golan Sifaniya, David Raya, wanda ya buga mata wasannin aro a bara daga Brentford.

Daukar Merino da Arsenal ta yi zai bai wa Mikel Arteta karin masu buga gurbin tsakiya da ya haɗa da Declan Rice da Jorginho da Thomas Partey da kuma Martin Odegaard.

Merino ya kwan da sanin gasar Premier League, wanda ya yi kaka ɗaya a Newcastle daga nan ya koma Real Sociedad a 2018.

A Sifaniya ya taka leda tare da Odegaard a 2019-20 a Real Sociedad, lokacin da ya buga wasannin aro daga Real Madrid.

Merino, ya buga wa Sifaniya wasa 28, wanda ya yi karawa 45 a dukkan fafatawa a bara da cin ƙwallo takwas.