Lewandowski ya fara cin kwallo a La Liga ranar bikin haihuwarsa

An wallafa

Robert Lewandowski ya fara cin kwallo a Barcelona a La Liga ranar da yake bikin cika shekara 34 da haihuwa.

Barcelona ta je ta doke Real Sociedad da ci 4-1 a wasan mako na biyu a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da suka fafata ranar Lahadi.

Tsohon dan wasan Bayern Munich ya fara cin kwallon a dakika 47 da fara tamaula, bayan da Alejandro Balde ya buga masa tamaula.

Real Sociedad ta farke ta hannun Alexander Isak a minti na shida da take leda.

Ousmane Dembele ne ya ci wa Barcelona kwallo na biyu, Lewandowski ya kara na uku na biyu da ya zura a raga a wasan, sannan Ansu Fati ya ci na hudu.

Nasarar farko da Barcelona ta yi a gasar La Liga ta bana, bayan 0-0 da Rayo Vallecano ranar 13 ga watan Agusta a Camp Nou.

Lewandowski ya koma Barca a bana daga Bayern Munich kan fam miliyan 42, bayan da yarjejeniyar kaka daya ta rage masa a kungiyar Jamus.

Wani sabon dan wasan da ta dauka a bana daga Leeds, Raphinha ya shiga wasan daga baya, amma bai ci kwallo ba.

To sai dai Barcelona ba ta sa mai tsaron baya Jules Kounde ba, wanda har yanzu ba ta yi masa rijista ba, sakamakon matsin tattalin arziki da take fama da shi.

Dan kwallon tawagar Faransa ya koma Camp Nou a bana daga Sevilla a cikin watan Yuni.

Barcelona tana mataki na biyar a teburin La Liga za kuma ta kara da Manchester City a wasan sada zumunta ranar Laraba.

Ranar Lahadi Barcelona za ta buga wasan mako na uku a gasar La Liga da Valladolid a Camp Nou.