Me ya sa darajar dala ke hauhawa?

Asalin hoton, Getty Images
Dalar Amurka ta kai karfin da ba ta taba kaiwa ba a cikin shekara 20 idan aka kwatanta ta da sauran manyan kudaden duniya.
Wannan na nufin dalar ta fi tsada a saye ta, kuma dala za ta iya sayen fan ko yuro ko yen mafi yawa idan aka kwatanta canjinsu. Wannan ya shafi harkokin kasuwanci da tattalin arzikin magidanta a duniya baki daya.
Ya karfin dalar yake?
Mizanin auna darajar dala(DXY) - wanda wannan shi ne ake auna darajar dalar a kan yawancin manyan kudaden duniya kamar su yuro, da fan da yen - darajar ta tashi da kashi 15 cikin dari a 2022.
Wannan na nufin dalar ta kai darajar da ba ta taba kaiwa ba a shekara 20.
Me ya sa dalar take da karfi?

Asalin hoton, Getty Images
Babban bankin Amurka ya kara yawan kudin ruwa na kasar sau da dama domin magance matsalar hauhawar farashin kaya. Wannan ya sa rancen kudi ya kasance da tsada sosai.
Wannan na nufin ke nan mutum zai samu riba sosai idan ya sayi kudaden lamuni da gwamnati ke sayarwa, wanda hakan ya sa masu zuba jari son sayen takardun lamunin na gwamnati wadanda ake kira ''Bond''
Su dai wadannan takardu na lamuni wata hanya ce da gwamnati ke rantar kudi daga kamfanoni ko 'yan kasuwa wadanda za ta biya nan gaba da karin kudin ruwa. Yawanci ana ganin ba su da wata matsala ko hadarin saye.
A watan Yuli na 2022 kadai masu zuba jari na waje sun sayi dala biliyan 10.2 daga gwamnatin Amurka, a dalilin haka a yanzu suna da dala tiriliyan 7.5.
Dole ne masu zuba jari su sayi dala domin samun damar sayen wadannan takardu na lamuni, ko wannan bukata ta neman dala ita ce za ta kara wa dalar daraja.
Saboda haka idan masu zuba jari suka sayar da takardun kudaden wasu kasashen domin su sayi dala, to wadancan kudade sai darajarsu ta ragu.
Darajar fan ta karu sosai lokacin da gwamnatin Birtaniya ta sanar da zaftare haraji.
Haka kuma masu zuba jari suna sayen dala a duk lokacin da tattalin arzikin duniya ke cikin matsi, saboda girman kudin na Amurka wannan ya sa suke zama wani tudun-mun-tsira. To wannan ma na sa darajar kudin na Amurka ta karu.
Kasashe da dama a Turai da Asia na fama da matsalar tattalin arziki saboda tashin farashin iskar gas abin da rikicin Ukraine ya haddasa.
Sai dai kuma wannan karfi na dala na cutar da kamfanonin Amurkar wadanda suke samun kudadensu daga sauran kasashen duniya, kamfanoni irin su Apple da Starbucks.
Ta yaya karfin dala ke shafar kudaden kasashen da ba su da kudi mai karfi?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kasashen da kudadensu ba su da karfi za su iya amfana da karfin dala saboda za ta sa kaya da ayyukan da suke sayar wa Amurka su yi araha, wanda hakan zai habaka cinikin da suke samu daga Amurkar
To amma kuma ta daya hannun karfin dolar zai sa kaya da ayyukan da ake saya daga Amurka su yi tsada.
Tun da da dala ake sanya farashin mai to karfin dala zai sa man ya yi tsada a kasashe da dama na duniya.
Misali a Kenya, finda kudin kasar wato Sulai (shilling) ya yi faduwar da bai taba yi ba a kan dala, farashin man fetur ya karu da kusan kashi 40 cikin dari tun farkon shekaran na ta 2022.
Gwamnatoci da kamfanoni a ƙasashe da dama kan karɓi bashi a dalar Amurka fiye da kuɗin ƙasarsu saboda ta fi tabbas.
Yayin da darajar dalar ke ƙaruwa, su kuma ƙasashen na ƙara fuskantar matsi wajen biyan bashin da kuɗin ƙasashensu.
Gwamnatin Argentina na cikin ƙasashen da suka fi shan wahala sakamakon ƙaruwar darajar dalar.
Ta haramta shiga da wasu kayayyaki cikin ƙasar, ciki har da jiragen ruwa na alfarma da giya da zummar kare darajar kadarorinta.
Yaya batun ma'aikata da ke aika dalar zuwa gida?

Asalin hoton, Bernadette Roque Cruz
A kowace shekara, ma'aikata a ƙasashen waje kan aika kuɗin da aka ƙiyasta sun kai dala biliyan 625 ga iyalansu a ƙasashensu na asali. Waɗanan kuɗaɗe za su iya yin matuƙar amfani ga tattalin arzikin ƙasashen.
Ma'aikatan ƙasashen waje a Amurka kaɗai kan aika dala biliyan 150 duk shekara; fiye da biliyan 30 zuwa Mexico, biliyan 16 ga China, biliyan 11 ga Indiya, biliyan 11 zuwa ga Philippines.
Girman darajar da dala ke da ita shi ne ke fayyace yawanta a sauran kuɗaɗen duniya. Hakan ya sa waɗanda ke samun saƙon kuɗaɗen a dala suka fi saura watayawa.
Bernadette Cruz na zaune tare da 'ya'yanta uku a birnin San Jose na Philippines.
Iyalin sun dogara ne kan dalolin da mijinta mai suna Fred ke aika musu daga birnin New York na Amurka, inda yake aiki a matsayin ma'aikacin jinya tsawon shekara 18.
Darajar dala ta ƙaru da kashi 13.5 cikin 100 kan kuɗin Philippines na peso. "Farashin kayayyaki baki ɗaya sun tashi a Philippines, ciki har da na kayan abinci da ƙwadago," a cewar Bernadette.
"Amma yawan darajar dala na taimaka min wajen sayen kayayyakin da muke buƙata. Abin da ya ɗoru a kan kuɗin na nuna irin sadaukarwar da mijina ke yi a ƙasar waje."
Me ƙasashe ke yi game da hauhawar darajar dala?
Ƙasashe da yawa a faɗin duniya na duba yadda za su haɓaka darajar kuɗaɗensu ta hanyar ƙara yawan kuɗaɗen ruwa.
A Argentina, kuɗin ruwand a babban bankin ƙasar ya saka ya kai kashi 69.5 cikin 100. A Ghana kuma kashi 19 ne, 14 a Najeriya, sai kuma 13 a Brazil.
A gefe guda, ƙara yawan kuɗin ruwa na nufin abu ne mai wuya ga iyalai su iya karɓar bashin kuɗi.
Kamfanoni za su sha fama, har ma ƙila su rage ma'aikata. Iyalai kuwa za su rage kashe kuɗi.
Sakamakon haka, wannan na iya jawo karayar tattalin arzikin ƙasashe.











