Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gwamnatin Najeriya ta bukaci a bude jami'o'i
Gwamnatin Najeriya ta umarci duk shugabannin jami'o'in kasar da ke karkashin kulawarta su koma bakin aiki tare da kyale dalibai su koma karbar darussa.
Wannan umarnin na zuwa ne bayan wata bakwai da aka shafe malaman jami'o'in gwamnatin tarayya na yajin aiki.
Gwamnatin Najeriya ta kai karar kungiyar malaman ta ASUU, inda a makon jiya kotun ta umarci malaman da su janye yakin aikin, sai dai kungiyar malaman ta daukaka kara, matakin da ka iya tsawaita wannan takaddama.
Wannan umarnin na bude jami'o'i na kunshe cikin wata takarda da hukumar kula da jami'o'in Najeriya, NUC ta aika wa shugabannin jami'o'i mallakan gwamantin tarayyar Najeriya, wadda babban sakataren hukumar ta NUC ya sanya wa hannu.
BBC ta gano cewa, Ministan Kwadago Dakta Chris Nigige ne ya mika hukuncin kotun ma'aikata ta Najeriya kai-tsaye ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu.
Daga nan ne Ministan Ilimin ya umarci a aiwatar da wannan matakin na bude jami'o'in, ta hannun ma'aikatar da ke kula da jami'o'in Najeriya NUC - matakin da shi ne aka aiwatar da safiyar yau Litinin.
Akwai kwafen wasikar a hukumar ta NUC wadda ta umarci shugabannin jami'o'i da su tabbatar cewa malaman jami'a karkashin kungiyar ASUU sun koma koyar da dalibai.
Farfesa Yakubu Ochefu, babban sakataren kwamitin shugabannin jami'o'in Najeriya, ya tabbatar wa BBC cewa sun karbi wannan umarni.
Ya ce “Lallai mun karbi umarnin sake bude jami'o'i ta hannun wata wasika da hukumar NUC ta aiko mana, wadda ke bayyana hukuncin da kotun ma'aikata ta yanke kan batun."
Ya kuma kara da cewa “Sai dai a halin yanzu muna tattaunawa ne tsakanin shugabannin jami'o'i da iyayen jami'o'in, domin gano yadda za mu iya aiwatar da umarnin ba tare da mun taka umarnin kotu ba.”
Tun dai tsakiyar watan Fabrairun bana kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ta tsunduma yajin aiki tana neman gwamnatin tarayya ta biya ma ta wasu bukatu, ciki har da na sake duba albashin da ake biyan mambobin kungiyar.
Bayan an shafe watanni ana kiki-kaka, sai gwamnatin Najeriya ta kai batun ga kotun ma'aikata ta kasar, kuma kotun ta yanke hukuncinta a makon jiya, inda ta umarci kungiyar ASUU ta janye yajin aikin.