Ko ya za ta kaya a wasan Man City da Real Madrid?

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City za ta kara da Real Madrid a wasan cike gurbi a Champions League ranar Talata a Etihad.
City ta kawo wannan matakin , bayan da ta kare a mataki na 22 a teburin gasar zakarun Turai da aka canja fasali daga kakar nan.
Ita kuwa Real Madrid mai Champions League na bara na 15 jimilla, ta kare a gurbi na 11 a teburi, wadda cikin wasa takwas ta ci biyar aka doke ta uku.
Wannan shi ne karo na biyar da za su kece raini tsakanin City da Real a kaka shida baya.
Tuni dai Real Madrid ta sanar cewar Lucas Vazquez ba zai yi wasan ba, sakamakon raunin da ya ji a La Liga da Atletico Madrid ranar Asabar.
Tun kafin nan kungiyar ta Sipaniya na fama da masu tsare mata baya da ke jinya da ya hada da Antonio Rudiger da Dani Carvajal da Eder Militao da kuma David Alaba.
A bara ne Real Madrid ta hana City ɗaukar Champions League na biyu a jere, wadda ta yi nasara a bugun fenariti a Etihad a zagayen kwata fainal.
Kafin nan City ta doke Real Madrid 4-0 a Etihad da kai wa zagayen karshe da cin 5-1 gida da waje a kakar 2022/23.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hakan ya sa City ta lashe Champions League, sakamakon nasara a kan Inter Milan da cin 1-0 a Istanbul a karon farko a tarihi - a kakar ce ta lashe kofi uku rigis.
Wannan shi ne karo na 13 da City za ta kece raini da Real Madrid a gasar ta zakarun Turai, inda ta Premier League ta yi nasara huɗu da canjaras biyar, Real ta ci wasa uku.
Karawar da suka yi a 2023/2024:
Champions League Ranar Laraba 17 ga watan Afirilu
- Man City 1 - 1 Real Madrid
Champions League Ranar Talata 9 ga watan Afirilu
- Real Madrid 3 - 3 Man City
City ta fuskanci kalubale a kakar nan, wadda kawo yanzu ta buga karawa 37 a dukkan fafatawa, sai dai ta yi nasara 18 da canjaras takwas aka doke ta karo 11.
A cikin watan Oktoba Tottenham ta doke City, wadda daga lokacin ta yi wasa 13 a jere da kyar da ci ɗaya daga ciki da canjaras uku, sauran doke ta aka yi.
Kawo yanzu ƙungiyar ta Etihad tana ta biyar a teburin Premier League da maki 41 iri ɗaya da na Newcastle ta shida.
Real Madrid kuwa ita ce ta farko a teburin La Liga da maki 50, bayan kammala karawar mako na 23 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Cikin wasa 37 da Real Madrid ta buga kawo yanzu a dukkan fafatawa a kakar nan ta yi nasara 25 da canjaras shida aka doke ta wasa bakwai.
Sauran wasannin da za a buga a Champions League:
Ranar Talata 11 ga watan Fabrairu
- Brest da Paris Saint-Germain
- Juventus da PSV Eindhoven
- Manchester City da Real Madrid
- Sporting da Borussia Dortmund
Ƴan wasan Real Madrid da za su fuskanci Manchester City
Masu tsare raga: Courtois, Lunin da kuma Sergio Mestre.
Masu tsare baya: Vallejo, Fran García, Mendy, Jacobo, Asencio da kuma Lorenzo.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Modrić, Tchouameni, Arda Güler, Ceballos da kuma Chema.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Mbappé, Rodrygo, Endrick, Brahim da kuma Gonzalo.










