Kalli yadda ake murna a Lebanon kan yarjejeniyar tsagaita wuta

Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
Kalli yadda ake murna a Lebanon kan yarjejeniyar tsagaita wuta
An wallafa

Dandazon mutane sun rika murna a Lebanon bayan cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah.

Mutane na nuna farin ciki yayin da wasu ke tababar ɗorewar yarjejeniyar.

Dubban ƴan ƙasar Lebanon sun fara komawa garuruwansu da ke kudanci, sai dai Isra'ila ta yi gargaɗin cewa har yanzu babu tabbacin tsaro a wasu yankunan.