Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dan wasan Tottenham Richarlison ya yi watsi da ta yin komawa Saudiyya
Richarlison ya ce yana son ci gaba da zama a Tottenham Hotspur bayan watsi da yayi da tayin da ya samu daga lig ɗin Saudiyya.
Dan wasan gaban Brazil ɗin me shara 27 ya koma Spurs ne daga Everton a 2022 kan kuɗi fan miliyan 60.
Richarlison ya ci kwallo 15 cikin wasa 66 da ya bugawa ƙungiyar, sai dai bai samu gidin zama ba a kakar da ta gabata ƙarƙashin kulawar Ange Postecoglou.
Richarlson wanda kwantaraginsa za ta ƙare a 2027, ya samu tayi mai yawa daga ƙungiyoyin Saudiyya.
Ya ce yana son ci gaba da zamansa a Ingila saboda ya ci gaba da ƙoƙarin da zai sa a rika kiransa wasanni a ƙasarsa Brazil.
"Na samu tayi masu yawa, amma burin ci gaba da bugawa Brazil da zama a Premier ya fi ƙarfi," in Dan wasan Brazil a tattaunawar da ya yi da ESPN.
Spurs na son ɗaukar ɗan wasan gaba a wannan kakar, kuma har sun kyalla ido kan dan wasan Bournemouth Dominic Solanke.
Ita ma Bournmouth na son ɗan wasan nata wanda ya ci mata kwallo 21 a wasa 42 da ya buga a bara, sai dai ba a ɗauke shi cikin tawagar Ingila ba da ta buga Euro 2024.
Bournmouth ta yi masa kudi fan miliyan 65 duk da cewa yana da sauran shekara uku a kungiyar kan kwataraginsa ta ƙare - Sai dai Tottenham ta yi masa tayi ƙasa da abin da aka yi masa kudi.