Zanna Bukar: Cikar adon 'yan birni

    • Marubuci, Badariyya Tijjani Kalarawi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Hausa
  • An wallafa

Zanna Bukar, hamshaƙiyar hula ce da ke ƙara samun ɗaukaka, musamman a tsakanin masu mulki da sarakuna da 'yan siyasa, kai har ma da matasa 'yan birnin billahillazi.

Ana yi wa Zanna Bukar, kallon hular ƙarshe ta adon cinyewa da fita kunya.

Hular, ta samo asali ne daga jihar Borno a arewa maso gabas - yankin daular Kanuri mai gawurtaccen mulkin sarauta da ɗumbin tarihi.

Rikicin ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram tsawon fiye da shekara goma, da abubuwan da ya haifar kamar yawan dokar hana fita, da hukumomi kan ƙaƙaba duk lokacin da aka kai wani babban farmaki a manyan birane kamar Maiduguri.

Ga kuma dubban ɗaruruwan mutanen da rikicin ya tarwatsa daga garuruwansu zuwa gudun hijira, duka sun haɗu sun taka rawa wajen ƙara ɗaukaka sana'ar ɗinka hula Zanna Bukar.

An yi amanna Alhaji Zanna Bukar Dipcharima, ministan Najeriya a jamhuriya ta ɗaya, shi ne ya fito da hular ta ƙara samun karɓuwa, ba kawai a Borno da kewaye ba, har a lardin arewa da ma faɗin Najeriya. Daga bisani sai sunan Dipchirima ya ɓata, ake kiran ta da Zanna Bukar kawai.

Ita ma, Amina Rawaram, wata fitacciyar mawaƙiya da ta shahara a zamaninta ciki jihar Borno, gudunmawarta wajen ƙara samun ɗaukakar Zanna Bukar, ba abin mantawa ba ne da wuri. Inkiyar mawaƙiyar dai ya bi hular, wadda wasu ke kiran ta da Rawaram.

Ɗinkin hula na cikin sana’o’in da mutane da dama ke cin abinci, kafin a ƙarshe ta je ga mai sayen da zai kafa a gaban goshi, ya fito yana ƙwambo.

Ɗinkin hula Zanna Bukar, na bin matakai da dama kafin ta kammala, a wanke, a naɗe, sannan a kai ta kasuwa.

Wani ƙiyasi na cewa mutane kamar 25 ne ke ba da gudunmawa wajen sarrafa duk hular Zanna Bukar da kuka gani an rangaɗa ado da ita, ana ƙwambo a birni. Kuma ita ce hanyar samun kuɗin shiga ga wannan rukuni na mutane.

Gwanin zane ne matakin farko na ɗinkin Zanna Bukar, sai kuma a je ga batun fitar da launukanta. Gwanar ɗinki daga nan sai ta zauna dirshen ta yi ta soka allura da zare wajen saƙa hular. Kafin ta kammala mai yin rufi na can yana nasa aiki, sai kuma a yi batun ƙoƙuwa.

Ana kuma yi wa Zanna Bukar shafi, da cin baki sannan ɗosana ƙwalli kafin a kai ta bugu, da sauransu.

Abu ne mawuyaci ka shiga gida a birnin Maiduguri, ba ka yi kiciɓis da masu ɗinkin hula ba, wasu lokatan akan samu iyalai gaba ɗaya, aikin da suke yi kawai kenan.

Irin wannan yanayi na sana'ar ɗinkin hula yana da ban sha'awa, musamman inda za ka iya samun maigida da matar gidan da 'ya'yansu zaune a rumfar tsakar gida, kowa ya duƙufa aikin hula.

Na ziyarci unguwar Bulaburin, wadda ta yi fice da sana'ar ɗinkin hula a birnin Maiduguri. Idan ka shiga gida biyar, kana iya samun uku a ciki, ko dai mata da 'yan mata ko tsofaffi suna ɗinkin hula.

Hajja Falmata Goni ta shaida min cewa tun tana matashiya take sana'ar ɗinkin hula. Ta ce ta koya wa 'ya'yanta maza da mata, kai har da surukanta sana'ar ɗinkin hula. Kuma a cewarta, ta samu tarin alhairai da ɗinkin hula.

Mutum na farko da maɗinkan hula kamar Hajja Falmata Goni ke tuntuɓa a duk lokacin da suka yanke shawarar fara aiki, shi ne mai zane.

Ni ma na dangana da wurin Mallam Abdullahi, ɗaya daga cikin masu wannan aiki a Bulaburin, inda na riske shi a bakin aiki yana yana zanen hula. Ya ce tun suna ƙanana suke raka mahaifinsu wurin aikinsa na yin zane, kafin shi ma Allah ya kai shi ga matsayin gwani a wannan fanni.

Da farko dai yakan yi amfani da biro da rula ta 'yan makaranta a wannan aiki na zane. Yakan fara da dogayen layuka sirara cike da ƙwarewa. Wani babban abin sha'awa shi ne ba za ka samu ko layi ɗaya ya karkace a aikinsa ba.

Mallam Abdullahi ya ce da wannan aiki zane na Zanna Bukar ya yi aure, kuma ya gina muhalli, da shi ne kuma yake samun abin kula da 'ya'yansa har guda uku.

Farashin kowanne zanen hula kan fara daga naira 500 zuwa sama, ya danganta da yawan zanen da ake buƙata, wanda yakan kammala cikin 'yan mintuna. A kullum yakan yi zanen hula 10 zuwa 20, amma idan kasuwa na garawa yana yin har fiye da hakan.

Daga nan kuma sai wanda zai fitar da launi ko kalar zaren da za a yi amfani da shi wajen ɗinkin hular, shi ma lamari ne mai girma ana amfani da maka launi daban-daban domin fitarwa.

Wannan ne tsarin da masu ɗinkin za su bi wajen sayen zare launin da ke jikin zanen, sai kuma a hau ɗinki.

Ingantacciyar hula na ɗaukar aƙalla mako biyu zuwa uku, wata ma har tsawon wata ɗaya kafin ɗinkin ta ya kammala.

Toluwar saman hular ita ce Bukar, ana dasa ta ne da zarar an ɗora rufi, a yi cin baki, a sanya mata ƙwalli, daga nan masu sanya sitati su ɗauka, sai mai bugu wanda shi ne ke sanya zanen ya fito fes cike da sheƙi, tana ɗaukar ido.

Matasan da ke samun kuɗin shiga ta hanyar ɗinkin hula a Maiduguri, suna da ɗumbin yawa. A cikinsu har da wata budurwa mai suna Fatima Muhammad. Ta shaida min cewa ta taso ne tana haɗa sana'a da karatu don samun rufin asirin rayuwa.

Ta dai ƙara da yi min bayani game da burinta a kan wannan sana'a: ''Hula ɗaya na ɗauka ta sati biyu zuwa uku, kuma ni kaɗai nake yin komai tun daga zane, na fitar da kala, na yi ɗinki, na rufa, na zo cin baki, har da ƙwalli."

Lokacin da nake zuwa makaranta, in ji ta, ina ware lokacin ɗinki daban, lokacin karatu ma haka, amma da na kammala sakandare ban ci gaba da zuwa makaranta ba, sai na mayar da hankali kan sana'ata.

"Dukkan bukatuna a ciki nake yi, har na taimaki wasu, kuma fatana nan gaba ina son bunƙasa sana'ar in zamanantar da ita, na buɗe makarantar da mata da 'yan mata za su koyi sana'ar domin abar rufin asiri ce.''

Zanen hular da adon jikinta suna sauyawa daga wata zuwa wata, gwargwadon inda guguwar yayi ta kaɗa, akwai nau’in Zanna Bukar sama da 50, kowacce da irin nata zanen.

Akwai mai dagin sarauta, akwai mai kusurwa huɗu, ana samun mai gatari da sauransu.

Wani zanen da ya shahara shi ne Amina Rawaram, fitacciyar mawakiya mai farin jini a zamaninta. Babba cikin fasalinta mai ɗaukar hankali shi ne zanen Gatari da akan yi wa ado da zare launin ruwan goro mai duhu, da kore da mai launin makuba, da fari wanda akan rufa hular da shi.

Wani ƙarin abin burgewa game da Zanna Bukar shi ne kowanne zane yana da sunansa, asali ma ana bai wa hulunan sunayen mashahuran mutane ne ko shugabanni da sarakuna, kuma ba lallai ‘yan asalin Borno ba.

Bunu Bukar da ya daɗe a wannan fanni, ya shaida min suna la'akari ne da yadda mashahuran mutane ke sanya hular, da zane ko kalar da suka fi so, har ma da salon karinsu.

''Kin ga dai a tsofaffin huluna muna da Zanna Bukar Dipchirima, Zanna Bukar Mandara, Amina Rawaram wannan sun kai 100."

"Akwai Kashim Shettima kala biyu, da wadda yake sanyawa zamanin yana gwamnan Borno da kuma ta yanzu a matsayinsa na mataimakin shugaban ƙasa."

Ya kuma ce akwai nau'in hular mai suna SAS da Mai Mala da Tunibu, akwai ma Zulum, suna da yawa gaskiya.

"Ba kuma lallai sai masu mulki muke sanyawa sunan hula ba, ya danganta da fice ko abin da mutum ya shahara a kai,'' in ji shi.

Sai dai babbar matsalar da masu wannan sana'a ke fama da ita, shi ne rashin tallafi don bunƙasa jari musamman daga gwamnati.

Madu Challu na cikin shugabannin maɗinka hula a Bulaburin: ''Abin da ya fi damunmu shi ne, rashin tsayayyar kasuwa ko inda za mu yi sana'armu."

"Kin ga wurin nan ya yi mana kaɗan, unguwa ce kawai ake amfani da ita.

"Amma da gwamnati za ta sama mana wuri kamar 'yan'uwanmu masu harkar wayar salula wato GSM Village, mu ma za mu ba da gudunmawa ta hanyar biyan haraji da ƙara samar da kuɗin shiga ga gwamnati."

Ya ce za su samu damar ƙara yawan masu sana'ar tun da akwai ɗumbin marasa aikin yi, kuma da yawan magidanta, da sana'ar suke ɗaukar ɗawainiyar iyalai, kama daga ciyarwa, biyan kuɗin makaranta da tufatarwa, da sauran bukatun yau da kullum.

"A nan kara zube muke, manyan da suka girme mu ko suka kai matsayin shugabanni, su ne kan tsawatar idan bukatar hakan ta taso."

Fama da mukai da ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram ya zama silar samun haɓakar sana'ar ɗinkin hula a Maiduguri, in ji Madu.

Za a iya cewa dai Mutane da dama kawai suna sa hula ne ba tare da sanin irin ƙumajin da aka yi kafin ta je kansu su fara kiran ta da suna Zanna Bukar ba.

Abin da ya rage a harkar sana’ar hula musamman yadda ta ratsa nahiyar Afirka, shi ne tabbatar da hakkin mallaka domin kange sana’ar daga masu satar fasaha da yanzu hula zanna bukar ke fuskanta.