Arsenal ta yi fintinkau a farautar Sesko, Kane na son komawa Ingila

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta sha gaban Tottenham a farautar ɗan wasan Slovenia, Benjamin Sesko mai shekara 21 daga RB Leipzig. (Football Insider)
Ɗan wasan gaba a Sweden Viktor Gyokeres mai shekara 26, ya nuna alamar son barin Sporting a wannan kakar. (Record - in Portuguese)
Liverpool da Arsenal na iya sayen Alexander Isak mai shekara 25, a lokacin bazara ba tare da karya ka'idojin kuɗaɗe ba, duk da farashin da Newcastle ta yi masa na fam miliyan 150. (Football Insider)
Liverpool na son ɗauko ɗan wasan Hungary, Milos Kerkez mai shekara 21 a lokacin bazara, yayinda Real Madrid ita ma ta shiga zawarcinsa. (Teamtalk)
Ɗan wasan tsakiya a Ingila Kobbie Mainoo mai shekara 19, na iya watsi da sabon tayi daga Manchester United domin komawa Ketare, kuma ƙungiyar na iya sayar da shi kan fam miliyan 70. (Guardian)
Harry Kane na iya koma buga Firimiyar Ingila a lokacin bazara domin Bayern Munich na duba yiwuwar barin ɗan wasan mai shekara 31 daga Ingila ya tafi bisa sharudan da aka cimma a kwantiragin da ya sanya hannu na sayar da shi kan fam miliyan 67. (Sun)
Newcastle na iya daidaitawa da ɗan wasan gaba a Porto da Sifaniya, Samu Aghehowa kan kuɗin da bai kai fam miliyan 82.5 ba, bisa sharudan yarjejeniyar da yake kai, ƙungiyoyin Arsenal da Aston Villa da West Ham na zawarcin matashin mai shekara 20. (Football insider)
Liverpool ta matsu ta saye ɗan wasan tsakiya a Stuttgart da Jamus, Angelo Stiller, mai shekara 23. (Bild via the Daily Briefing - in German)
Manchester United na neman kofa domin raba gari da ɗan wasan tsakiya a Brazil , Casemiro mai shekara 33. (Teamtalk)
Ɗan wasan gaba a Canada Jonathan David mai shekara 25, na son tafiya Ingila a wannan kaka idan kwantiraginsa ya kare a Lille, kuma Manchester United da Tottenham da Chelsea da Newcastle duk sun kwaɗaitu. (Caught Offside)
Juventus na nazari kan ɗan wasan Atalanta da Brazil, Ederson mai shekara 25, da kuma ɗan wasan gaba a Najeriya Ademola Lookman mai shekara 27, da mai taka leda a Italiya, Mateo Retegui mai shekara 25. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)
Manchester City ta amince ta biya Hibernian fam dubu 235,000 kan mai tsaron ragarsu ɗan makaranta, Ben Vickery mai shekara 15. (Manchester Evening News)











