Marseille ta ɗauki Rabiot a matakin wanda bai da ƙungiya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan tawagar Faransa, Adrien Rabiot ya koma Marseille mai buga Ligue 1 a matakin mara ƙungiya.

A karshen watan Yuli yarjejeniyar Rabiot ya kare a Juventus mai buga Serie A.

Mai shekara 29 ya yi karawa biyar a Euro 2024 a gasar da Faransa ta kai daf da karshe.

An bayar da rahoton cewar ƙungiyoyi da yawa sun yi kokarin sayen ɗan wasan kan fara kakar bana har da wasu daga Premier League harda Manchester United.

Rabiot ya taka leda a makarantar koyon tamaula ta Manchester City daga baya aka sayar da shi ga Paris St Germain, wadda ya fara buga wa tamaula a matakin ƙwararren ɗan ƙwallo.

Tsawon wasannin da ya taka leda a babban birnin Faransa ya lashe kofi 18 ciki har da Ligue 1 guda biyar daga ciki.

Rabiot ya koma Juventus a 2019/20 da lashe Serie A a kakar farko a birnin Turin daga nan ya ɗauki Italian Cup biyu da Italian Super Cup.

Marseille tana ta biyu a teburin Ligue 1 a bana, wadda ta haɗa maki 10 daga karawa huɗu karkashin sabon kociyan Roberto de Zerbi.